An ba hafsoshin tsaro N238bn don siyan makamai cikin shekaru biyu - Rahoto

An ba hafsoshin tsaro N238bn don siyan makamai cikin shekaru biyu - Rahoto

Bincike ya tabbatar da cewa, ma'aikatar tsaro ta samu fiye da naira biliyan 238 domin mallakar makaman yaki a shekarar 2018 da kuma 2019 kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Ma'aikatar tare da hedikwatar dakarun soji da suka hadar da na kasa, sama da kuma na ruwa, sun samu wannan makudan kudi domin tabbatar da inganci tsare-tsare da manufofi na yaki da ta'addanci.

Hakan yana kunshe cikin alkaluman da ofishin kasafin kudi na fadar gwamnatin tarayya ya fitar kan shafinsa na yanar gizo a ranar Alhamis.

Rahoton da ofishin kasafin kudin ya fitar, ya nuna cewa, ma'aikatar tsaro da kuma hedikwatar rundunar dakarun sojin Najeriya, sun fitar da kasafin naira biliyan 316 domin al'amuransu na gudanarwa a shekaru biyun da suka gabata.

Gwamnatin tarayya ta danka musu naira biliyan 238 wanda ya kasance kashi 75 cikin 100 na adadin kasafin kudin da suka nema.

A tsakanin wannan lokacin, ta'addancin mayakan Boko Haram, fashi da makami da sauran tashe-tashen hankali a kasar ya hauhawa, kuma akalla sojoji 71 sun rasa rayukansu a hannun 'yan ta'adda a tsakanin Janairu zuwa Yulin 2020 kadai.

Hafsoshin tsaro na Najeriya
Hafsoshin tsaro na Najeriya
Asali: UGC

Legit.ng ta fahimci cewa, duk da wannan makudan kudi da gwamnatin tarayya ta tanada domin hukumomin tsaro na kasar, ta'addanci ya ci gaba da ta'azzara a fadin kasar musamman a Arewacin Najeriya.

Jaridar ta ruwaito cewa, a ranar Talata ne Majalisar Dattawa ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro na ƙasar su sauka daga mukamansu saboda ci gaba da tabarbarewar tsaro a ƙasar.

Majalisar ta cimma wannan matsayin ne bayan Sanata Ali Ndume, (APC, Borno) ya gabatar da kudirin nuna damuwarsa kan rahoton murabus ɗin da sojoji fiye da 200 suka yi.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 16 a Abuja da Neja

'Yan majalisar da suka tofa albarkacinsu a kan kudirin da Ndume ya gabatar sun koka kan yadda lamuran tsaro ke cigaba da tabarbarewa da kuma rashin iya gudanar da ayyukan ci gaba a yankunan.

Sun ce jamian sojoji da dama suna tsoron rasa rayyukansu yayin yaki da taadancin hakan yasa suke barin aikin da kansu.

Mataimakin shugaban kwamitin kwastam, Sanata Ayo Fadahunsi ya bayar da shawarar shugabanin tsaron su yi murabus inda Sanata Betty Apiafi ta goyi bayansa.

Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan shima ya amince da bukatar kuma sanatoci da dama da suka hallarci zaman suma sun amince.

Majalisar ta kuma bukaci kwamitin ta na tsaro ta binciko dalilin da yasa jami'an sojojin suke yin murabus da kansu.

A jawabinsa, Sanata Lawan ya ce duk da cewa rundunar sojojin tana iya ƙoƙarin ta don samar da tsaro, ƙoƙarin nata bai wadatar ba saboda haka ya yi kira ga Shugaba Buhari ya nada sabbi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel