An kama ɗan Fasto da wasu mutum 5 da ake zargi da yi wa 'yar shekara 12 fyaɗe

An kama ɗan Fasto da wasu mutum 5 da ake zargi da yi wa 'yar shekara 12 fyaɗe

Yaron wani Fasto da wasu mutane biyar da ake zargi da aikata fyade, a yanzu haka an garkame su a dakin ajiye masu laifi na ofishin rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom da ke birnin Uyo.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, CSP N-Nudam Fredrick, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a karshen mako.

Ya ce duk mutane shidan da ake zargi sun amsa laifin biyan bukatarsu ta sha'awa da budurwa matashiya mai kananan shekaru.

A rahoton da jaridar Vanguard ta ruwaito, ababen zargin sun shiga hannu ne bayan an shigar da korafi ga ofishin 'yan sandan kan ta'asar da suka aikata.

A cewar CSP Fredrick, kwamishinan 'yan sanda na jihar Edgar Imohimi, ya lashi takobin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwato hakkin matan da aka ketawa haddi.

Kwamishinan 'yan sandan Akwa Ibom; CP Edgar Imohimi
Kwamishinan 'yan sandan Akwa Ibom; CP Edgar Imohimi
Asali: UGC

Ya nakalto kwamishinan 'yan sandan yana shawartar duk wadanda suka fada tarkon fyade, a kan kada su ji tsoro ko kunyar shigar da kara domin a nema musu hakki.

CP Imohimi ya kuma yabawa hukumar shari'a ta jihar dangane da yadda ta ke gaggauta zartar da hukuncin kan miyagun mutane masu ta'adar fyade.

Ya kara da cewa, masu irin wannan mugun hali ba za su taba samun wani sukuni ko wata nutsuwa ba matukar sun shiga hannu.

Wani rahoto mai nasaba da wannan da Legit.ng ta ruwaito, rundunar ‘yan sandan Najeriya sun wanke shararren Mawakin nan wanda aka sani da D’Banj daga zargin da wata Seyitan Babatayo ta yi masa na yi mata fyade.

A wani jawabi da ‘yan sanda su ka fitar ta bakin DCP Umar Sanda a madadin mataimakin sufeta janar na kasa wanda ke lura da binciken laifuffuka, an yi fatali da wannan zargi.

KARANTA KUMA: Ba za mu biya N60,000 ga masu cin moriyar N-Power ba - Gwamnatin Tarayya

Kamfanin dilllacin labarai na kasa, NAN ya ruwaito cewa, ofishin FCID na ‘yan sandan ya na cewa babu hujjar da ke nuna Tauraron ya yi lalata da Seyitan Babatayo da karfin tsiya.

Sanarwar ta bayyana cewa, Miss Seyitan Babatayo ta jefi D’Banj da zargin yi ma ta fyade da kokarin yi wa maganar rufa-rufa.

Ko da cewa Seyitan ta yi wasa a wannan otel, jami’an ‘yan sanda sun ce babu abin da zai nuna Oladapo Daniel Oyebanjo ya yi lalata da ita, don haka aka kashe maganar.

DCP Sanda ya ce bincike ya nuna babu gaskiya a korafin da Seyitan Babatayo ta yi na cewa Oladapo Daniel Oyebanjo watau D’Banj ya yi amfani da ita ba tare da iznin ta ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel