Ainihin dalilin da ya sa aka hana 'yan Najeriya samun aiki a Dubai

Ainihin dalilin da ya sa aka hana 'yan Najeriya samun aiki a Dubai

A baya bayan nan 'yan Najeriya suka bayyana takaici a zaurukan sada zumunta biyo bayan wani tallan neman ma'aikata a Dubai da ya nuna cewa ba a bukatar 'yan Najeria su nemi aikin domin ba za su samu ba.

Kamfanoni a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE sun fara tsame 'yan Najeriya daga cikin jerin mutanen da za su dauka aiki bayan da aka kama Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Idan ba a manta ba, an damke Hushpuppi da wasu 'yan Najeriya da ake zargi da laifin damfara a Dubai kuma aka mika su Amurka.

Legit.ng ta ga wasu tallace-tallace a yanar gizo na neman daukan ma'aikata a Dubai inda aka bayyana karara cewa banda 'yan Najeriya a wadanda ake bukata.

Dubai
Dubai
Asali: UGC

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, tallan ya kuma ce "'yan Afirka maza ko mata na iya neman aikin amma ban da 'yan Najeriya."

Bayan nan, an fara hana 'yan Najeriya Visa zuwa yawon bude ido a kasar.

A wasikar da Legit.ng ta gani, kasar ta sanar da 'yan Najeriya masu fasfotinta cewa, bata amince su samu hatimin shiga kasar ba don yawon bude ido na wannan lokacin.

"Mun gode da ku ka tuntubemu. Amma muna takaicin sanar da ku cewa ba a amince ba saboda duk 'yan Najeriya da ke da fasfotin kasar, ba a aminta da basu damar shiga UAE ba don yawon bude ido.

"Amma kuma, akwai yuwuwar hakan ta sauya a kowanne lokaci," wasikar tace.

Sai dai 'yan Najeriya mazauna Dubai yayin zantawa da manema labarai na jaridar The Nation sun ayyana cewa, tsame 'yan Najeriya daga cikin masu samun aiki a kasar ba ya da nasaba da harkallar Hushpuppi.

A cewarsu, daina daukar 'yan Najeriya aiki ya dade da fara tasiri tun gabanin lamarin Hushpuppi ya bayyana.

KARANTA KUMA: An yi bikin yaye tubabbun 'yan Boko Haram 601 a jihar Gombe

Wani dan Najeriya mazauni a Dubai, Femi Johnson, ya ce shawarar da aka yanke na tsame 'yan Najeriya daga cikin sahun masu samun aiki a Dubai ba ta gwamnatin UAE ba ce illa iyaka ta wasu kamfanoni masu zaman kansu.

"Ya ce 'yan Najeriya da dama na son bin hanya mai sauki. Misali, sayar da giya an tsara shi a nan amma wasu 'yan Najeriya sai sun kaucewa hanyar da ta dace wajen nuna su masu wayo ne."

"A Juma'ar da ta gabata, wasu 'yan Najeriya sun hada casu a yankin Sharja kuma suka shiga takun saka da hukuma."

"Wani makwabcinsu dan kasar Indiya, ya nemi su rage karar sautin kidin da suka sanya amma suka yi banza da shi."

"Bayan musayar yawu ta kaure a tsakaninsu, suka jefo mutumin daga ginin mai hawa 14, lamarin da ya sa 'yan sanda suka shigo suka kama' yan Najeriya da sauran 'yan Afirka da ke wurin."

Irin wannan lamari a cewar Johnson, shi ke sa wa ana yanke ƙauna ga 'yan Najeriya tare da shafawa wadanda basu ji ba kuma basu gani ba bakin fyanti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel