Gwamnatin Kaduna ta rufe otel, kantina da gidajen cin abinci saboda karya dokar COVID-19

Gwamnatin Kaduna ta rufe otel, kantina da gidajen cin abinci saboda karya dokar COVID-19

- Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wasu kantina, otel da gidajen cin abinci

- Ma'aikatar bunkasa kasuwanci da fasahar cinikayya ta jihar Kaduna ce ta rufe gine ginen a wani rangadi da tayi a ranar Juma'a a fadin jihar

- Gwamnatin jihar ta ce ba zata yi wata wata ba wajen hukunta duk masu kasuwancin da suka ki bin dokokin kariya na COVID-19 da aka sanya a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Nasir Elrufai ta rufe wasu otel otel, kantina da gidajen cin abinci saboda karya dokar kariya ta COVID-19 sakamakon bude wuraren kasuwancinsu.

Gine ginen da aka rufe sun hada da otel otel, wuraren shan giya, wuraren cin abinci, wuraren hada buredi da wuraren yin wanka.

Ma'aikatar bunkasa kasuwanci da fasahar cinikayya ta jihar Kaduna ce ta rufe gine ginen a wani rangadi da tayi a ranar Juma'a a fadin jihar.

A yayin ran gadin, kwamitin ma'aikatar, bisa jagorancin kwamishinan ma'aikatar, Idris Nyam sun ci karo da kwastomomi suna cin abinci a wuraren cin abinci, gasa buredi da shan giya a wasu otel otel.

KARANTA WANNAN: FG - Kowacce jiha za ta samu tallafin miliyan 100 don dakile yaduwar COVID-19

Sauran dokokin da otel otel da wuraren cin abincin suka karya sun hada da rashin kiyaye tazara, rashin sanya sinadarin wanke hannu dana kashe kwayoyin cuta da kuma kin sanya makarin fuska.

Saboda karya dokar COVID-19: Elrufai ya rufe wasu otel otel da wuraren cin abinci
Saboda karya dokar COVID-19: Elrufai ya rufe wasu otel otel da wuraren cin abinci
Asali: Twitter

Kwamishinan ya yi gargadin cewa gwamnati ba zata yi wata wata ba wajen hukunta duk masu kasuwancin da suka ki bin dokokin kariya na COVID-19 da aka sanya a jihar.

Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya shaida cewa kowacce jiha daga cikin jihohi 36 na Nigeria da kuma babban birnin tarayya Abuja (FCT), za ta samu naira miliyan 100, domin ci gaba da yakar cutar COVID-19.

Mr Ehanire ya bayyana hakan a taron mako mako na kwamitin yaki da cutar na fadar shygaban kasa (PTF) a ranar Alhamis, a fadar shugaban kasa.

"Ina mai sanar da ku cewa kowacce jiha tare da babban birnin tarayya Abuja zata samu tallafin yaki da cutar COVID-29 ta hannun shirin bunkasa yaki da cututtuka (REDISSE).

"Da wannan tallafin, kowacce jiha da ke a Nigeria zata samu tallafin naira miliyan 100 domin dakile yaduwar cutr. Da zaran an kaddamar da tallafin asusun BHCPF zai fara aiki," a cewarsa.

Bankin Duniya ne ya samar da shirin REDISSE domin tallafawa duk kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS, a lokacin da aka fara yakar cutar Ebola tsakanin 2014 zuwa 2015.

Shirin na taimakawa kasashen wajen basu damar yin hadaka, domin cike gurbin matsalolin yaduwar cututtuka da kuma barkewarsu a kasashen Afrika ta yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel