Wata kwamishiniyar gwamna Obaseki ta yi murabus

Wata kwamishiniyar gwamna Obaseki ta yi murabus

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu daga jaridar The Nation na nuni da cewa kwamishiniyar jihar Edo, a ma'aikatar muhalli da tattalin kayan gwamnati, Dame Omoua Oni-Okpaku, ta yi murabus. Har yanzu ba a san dalilin murabus din nata ba.

Daga jihar Edo, kwamishiniyar jihar Edo, a ma'aikatar muhalli da tattalin kayan gwamnati, Dame Omoua Oni-Okpaku, ta yi murabus.

Oni-Okpaku ta yi murabus kusan wata daya bayan da kwamishinan watsa labarai da wayar da kai na jihar, Paul Ohonbamu ya mika tasa takardar murabus din.

KARANTA WANNAN: FG: Kowacce jiha za ta samu tallafin miliyan 100 don dakile yaduwar COVID-19

Duk da cewa har yanzu ba a sanar da murabus din Oni-Okpaku a hukumance ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, sai dai hadinimarta ta tabbatar da hakan ga jaridar The Nation.

Sai dai hadimar ta ki bayyana dalilin da ya sa kwamishiniyar ta yi murabus.

A watan Afrelu, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar Edo, Chief Taiwo Akerele, ya yi murabus.

Ya mika takardar murabus din nasa ga gwamnan jihar Godwin Obaseki, yana mai bayyana dalilinsa da cewar akwai rufa rufa a cikin gudanar da ayyukan gwamnatin.

A wani labarin; Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya shaida cewa kowacce jiha daga cikin jihohi 36 na Nigeria da kuma babban birnin tarayya Abuja (FCT), za ta samu naira miliyan 100, domin ci gaba da yakar cutar COVID-19.

Mr Ehanire ya bayyana hakan a taron mako mako na kwamitin yaki da cutar na fadar shygaban kasa (PTF) a ranar Alhamis, a fadar shugaban kasa.

"Ina mai sanar da ku cewa kowacce jiha tare da babban birnin tarayya Abuja zata samu tallafin yaki da cutar COVID-29 ta hannun shirin bunkasa yaki da cututtuka (REDISSE).

"Da wannan tallafin, kowacce jiha da ke a Nigeria zata samu tallafin naira miliyan 100 domin dakile yaduwar cutar.

Da zaran an kaddamar da tallafin asusun BHCPF zai fara aiki," a cewarsa.

Bankin Duniya ne ya samar da shirin REDISSE domin tallafawa duk kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS, a lokacin da aka fara yakar cutar Ebola tsakanin 2014 zuwa 2015.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel