Coronavirus: Babu Sallar idin babbar Sallah bana- Gwamnatin Kwara

Coronavirus: Babu Sallar idin babbar Sallah bana- Gwamnatin Kwara

Gwamnatin jihar Kwara ta soke idin babbar sallar 2020 a fadin jihar.

Gwamnatin tace ta dauki wannan mataki ne bayan hauhawar adadin masu cutar korona a jihar.

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan covid 19 na jihar, Kayode Alabi ya bayyana wa manema labarai a birnin Illorin, yace an dauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da kungiyar malamai da kuma Sarkin Illorin.

Alabi, Wanda kuma mataimakin gwamnan jihar ne yace: "Za a yi sallar jumaa kamar yadda aka saba tare da bin dokar nesa nesa da juna da kuma amfani da takunkumin rufe fuska.

Coronavirus: Babu idin babbar sallah- Gwamnatin Kwara
Coronavirus: Babu idin babbar sallah- Gwamnatin Kwara
Asali: Facebook

"Za’a rufe dukkan shaguna, kasuwanni, shoprite da wuraren wasanni a ranar sallah da washegarin sallah. Sannan zaa kuma rufe Zoo din jami'ar IIorin shima na kwanaki biyun.

"Bayan tattaunawa da shugabannin kungiyar kiristoci na Nigeria, gwamnati ta soke duk wani tsayuwar adduar dare na kirista.

"Adduoin coci kar ta wuce sa'a biyu tare da bin dokokin kariya daga cutar.

"Gidan rawa, gidan giya da makamancinsu zasu cigaba da kasancewa a rufe. Sannan kar ya kasance an samu mutum fiye da hamsin a wurin.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel