Bayan sa'o'in da aka shafe ana sulhu, Buhari ya dawo daga kasar Mali

Bayan sa'o'in da aka shafe ana sulhu, Buhari ya dawo daga kasar Mali

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Mali da yammacin ranar Alhamis, bayan sa'o'in da suka kwashe suna taron sirri don sasanta rikicin siyasa da ya barke a kasar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, taron ya samu halartar shugaban kasa mai masaukin baki, Boubacar Keita, shugaban kasa Machy Sall na kasar Senegal, Nana Akufo-Addo na Ghana da Alassane Ouattara na kasar Cote d'Ivoire.

Wata kungiyar tawaye mai suna M5 na jaddada cewa sai an watsa kotun kundin tsarin mulkin kasar, kuma shugaban kasar yayi murabus kafin dawowar zaman lafiya a kasar.

Rikicin ya barke ne bayan da kotun ta soke sakamakon zaben kujerun 'yan majalisa 31 da aka yi kwanan nan inda ta mika nasara ga wasu daban, wanda kungiyar adawar ta ce mutanen shugaban kasa Keita ne.

Rikici ya barke a ranar 10 ga watan Yuli wanda ya janyo jami'an tsaro suka kashe wasu daga cikin masu zanga-zangar. Hakan kuwa yasa rikicin ya sake barkewa har aka kasa shawo kanshi, wanda dole yasa ECOWAS ta shiga.

A wata takardar da Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan fannin yada labarai ya fitar a ranar Juma'a, ya ce shugabannin ECOWAS sun saurari bayani daga bakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma shugaban kungiyar adawar, Imam Mahmoud Dicko.

Kamar yadda yace, wakilan adawar da wata kungiya sun yi jawabi ga shugabannin ECOWAS yayin taron.

"Shugaban kasa mai masaukin baki ya yi jawabi ga shugabannin kasa da gwamnati a kan al'amuran siyasar kasar ballantana rashin jituwa da ke tsakaninsu da kungiyar adawar wanda hakan ya kawo zanga-zangar da rikici," Adesina yace.

Bayan sa'o'in da aka shafe ana sulhu, Buhari ya dawo daga kasar Mali
Bayan sa'o'in da aka shafe ana sulhu, Buhari ya dawo daga kasar Mali. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: El-Rufai ya amince da yin sallar Idi a Kaduna, ya bada sharudda 2

A yayin zantawa da manema labarai a kan abinda suka tattauna a taron, shugaban kungiyar shugabannin kasa da kuma gwamnatocin da ke karkashin ECOWAS, shugaban kasa Mahamadou Issoufou, ya ce kungiyar za ta yi duk abinda ya dace don ganin karshen rikicin Malin.

Issoufou, wanda shine shugaban kasar jamhuriyar Nijar, ya ce za a yi taron yanar gizo na shugabannin kasashen da ke karkashin ECOWAS a ranar 26 ga watan Yuli, don ci gaba da tattaunawa a kan lamarin tare da fatan za a samo maslaha.

Ya ce, tuni shugabannin kasashen suka amince da cewa za a yi duk abinda ya dace wajen ganin dawowar zaman lafiya tare da nagartar kasar.

Ya kara da cewa, barin rikicin siyasa ya mamaye kasar Mali zai shafi tsaron kasashen Afrika ta yamma ballantana masu makwabtaka da ita.

Shugaban ECOWAS ya jinjinawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a kan yadda ya amince da jagorancin sasanci tare da bincike a kan lamarin. Ya jinjinawa dukkan shugabannin kasashen Afrika ta yamma da suka halarci taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel