COVID-19: Sama da malamai 100,000 basu iya ciyar da kansu - NAPST

COVID-19: Sama da malamai 100,000 basu iya ciyar da kansu - NAPST

Shugabannin kungiyar malaman makarantu masu zaman kansu ta kasa, sun tabbatar da cewa a kalla malamai 100,000 da ke koyarwa a makarantun kudi basu iya ciyar da kansu ballantana iya biya wa kansu bukatun rayuwa saboda rufe makarantun da aka yi fadin kasar nan.

Shugaban NAPST, Kwamared Akhigbe Olumhense, wanda ya zanta da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi tare da masu rufin asiri da su duba halin da malaman makarantun kudi ke ciki a kasar nan.

Olumhense ya kara da cewa makarantu masu zaman kansu a fadin kasar nan sun kammala shirin budewa amma na gwamnati sun nuna rashin shirinsu.

Ya ce: "Abin takaici ne yadda cutar korona ta saka malaman makarantun kudi a mugun hali a fadin kasar nan.

"Da yawa daga cikin malaman makarantun sun samu albashinsu na karshe ne a watan Fabrairun 2020."

Ya ce rufe makarantu na zangon karshe na wannan shekarar na nufin cewa ba za a biya kudin makaranta ba, kuma hakan na nuna cewa babu albashin da za a biya malaman.

"Malaman makarantun kudi na fuskantar matsin rayuwa don a yanzu babu ranar bude makarantu," yace.

Olumhense ya bayyana cewa, an samu jerin sunayen malaman makarantun kudi 10,300 da aka mika gaban ma'aikatar ilimi don su samu kayayyakin rage radadi.

COVID-19: Sama da malamai 100,000 basu iya ciyar da kansu - NAPST
COVID-19: Sama da malamai 100,000 basu iya ciyar da kansu - NAPST. Hoto daga Tribune Online
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kasashe 10 na Afrika da ke da asibitoci da tsarin kiwon lafiya masu inganci

A wani labari na daban, Akin Abayomi, kwamishinan lafiya na jihar Legas, ya ce gwamnati na kashe tsakanin N500,000 zuwa N1 miliyan a kan kowanne mai cutar korona a jihar idan ta tsananta.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Abayomi ya ce yawan kudin da ake kashewa majinyatan cutar ya danganta ne da tsananin da cutar ta yi.

Kwamishinan ya ce suna kashe kusan N100,000 ga majinyacin cutar da bata yi wa tsananin kamu ba.

"Domin maganin cutar ga wanda bata tsananta ba ko take tsaka-tsakiya a cibiyar killacewa, muna kashe N100,000 a rana daya," Abayomi yace.

"Wannan kawai zai iya baku damar kintatar yawan kudin da gwamnatin ke kashewa a kan cibiyar killacewa da kuma magani tare da jinya.

"Idan kana bukatar kulawa sosai ko halin da majinyaci yake ciki ya tsananta, muna iya kashe N500,000 har zuwa miliyan daya a rana daya, duk hakan ya dogara da yadda cutar ta kama mutum ne.

"Kana bukatar abun taimakawa numfashi ne, wankin jini, magunguna. A gaskiya akwai matukar wahala a ce an gane nawa majinyacin da cutar ta kama sosai ya ci.

"Muna dai kokarin ganewa kuma za mu sanar da ku idan muka kammala," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel