Shekaru 62: Tsohuwar kwamishiniyar watsa labarai ta Nasarawa ta bakunci lahira

Shekaru 62: Tsohuwar kwamishiniyar watsa labarai ta Nasarawa ta bakunci lahira

Iyalan Mrs Titi-Victoria Monde, tsohuwar kwamishiniyar watsa labarai ta jihar Nasarawa, sun sanar da mutuwarta a safiyar ranar Alhamis. Mrs Titi-Victoria ta mutu tana da shekaru 62 a duniya.

Mr Paul Abuga, kani ga Monde, ya bayyana labarin mutuwarta ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a Akwanga, karamar hukumar Akwanga da ke jihar.

Abuga, wanda shine sakataren karamar hukumar Nassarawa Eggon, ya ce Monde, wacce kuma ta kasance shugabar kwalejin ilimi ta Akwanga, ta mutu ne a babban asibitin Akwanga.

"Allah ya jikan ruhin yayata da kuma wadanda suka rigamu gidan gaskiya cikin salama da sunan Allah, Amen," a cewarsa.

NAN ta ruwaito cewa Monde ta rike mukamin kwamishiniyar watsa labarai ta jihar a shekarar 2011 karkashin mulkin tsohon gwamnan jihar Tanko Al-Makura.

A wani labarin kuma; gwamnatin Nigeria ta bayyana cewa maganin gargajiya da kasar Madagascar ta sarrafa ba ya wani tasiri akan cutar COVID-19 sabanin yadda ake kuranta shi.

Ministan kiwon lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya bayyana hakan a Abuja a bitar da kwamitin dakile yaduwar Coronavirus take yiwa shugaban kasa kan halin da ake ciki.

KARANTA LABARIN: Maganin Madagascar baya warkar da cutar COVID-19 - Gwamnatin tarayya

Shekaru 62: Tsohuwar kwamishiniyar watsa labarai ta Nasarawa ta bakunci lahira
Shekaru 62: Tsohuwar kwamishiniyar watsa labarai ta Nasarawa ta bakunci lahira
Asali: UGC

A cewarsa, cibiyar bincike da bukasa magunguna ta Nigeria (NIPRD) ta fitar da rahotonta na karshe kan maganin gargajiya da kasar Madagascar ta samar.

Kuma rahoton ya bayyana cewa sinadaran da aka hada maganin iri daya ne da sinadaran da ke cikin itaciyar Tazargade.

"A lokacin da aka yi bincike, an ga cewar yawan shan maganin na rage tari, amma bai nuna cewar yana maganin cutar COVID-19 kamar yadda ake shelantawa ba.

"Sai dai, zamu ci gaba da zage damtse wajen bin hanyoyi na gano maganin cutar Coronavirus," a cewar Ehanire.

Ministan ya ce yawaitar sabbin masu dauke da cutar da ake samu a makonnan ya haura daga 500 zuwa 700, inda awanni 24 da suka wuce aka samu sabbin mutane 543 dauke da cutar.

A halin yanzu, mutane 38,344 ne ke dauke da cutar COVID-19 a Nigeria, inda kuma mutane 15,815 suka warke daga cutar bayan da akayi masu magani har aka sallamesu.

"A wannan halin, mun rasa mutane 813, inda muka tattara alkaluman mutanen da aka yiwa gwajin gaba daya zuwa 247,825."

"Bisa ga karuwar mutanen da muke samu, zamu iya cewa, akwai masu dauke da cutar da yawa a cikin al'umma, kenan, akwai yiyuwa karuwar wadanda zasu kamu," a cewar Ministan.

Sai dai ya jinjinawa jajurtattun 'yan Nigeria, wadanda aka gwadasu kuma aka same da cutar amma suka fito suka bayyanawa jama'a domin dakile yaduwar cutar.

Ya ce wadanda suka damu da kasar ne suka fito suka nunawa duniya cewa ba abun kunya bane ko abun boyewa don ka kamu da COVID-19, kuma sun nuna yardarsu ga kiwon lafiya na kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel