Majalisar wakilai za ta binciki 'batan dabo' da N100bn ta yi ta inganta arewa maso gabas

Majalisar wakilai za ta binciki 'batan dabo' da N100bn ta yi ta inganta arewa maso gabas

Majalisar wakilai ta ce za ta fara bincikar hukumar kula da ci gaban yankin arewa maso gabas (NEDC) a kan zargin waddaka da kudi har N100 biliyan.

An yanke wannan hukuncin ne bayan da Ndudi Elumelu, shugaban marasa rinjaye ya mika bukatar gaban majalisar a ranar Alhamis.

An kafa hukumar a shekarar 2017 don habaka jihohin da ta'addanci ya shafa a yankin arewa maso gabas.

A yayin mika bukatar, Elumelu ya ce an bai wa hukumar naira biliyan dari daga asusun gwamnatin tarayya amma sun yi 'batan dabo' ba tare da ganin wani abu da aka aikata dasu ba.

Dan majalisar mai wakiltar jihar Delta, ya zargi Mohammed Goni Alkali, manajan daraktan hukumar da bada kwangilolin da basu wanzu ba.

"Gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar naira biliyan dari amma a cikin shekara daya tak sun yi batan dabo ba tare da aikin a zo a gani ba.

"Babu aikin da aka yi wa 'yan gudun hijira ko kuma wani abun more rayuwa da ci gaba da hukumar ta yi wa yankin arewa maso gabas," yace.

"Abubuwan da ke cike da rashawa wadanda ake zargin manajan daraktan hukumar, Mohammed Goni Alkali da su sun hada da: bada kwangiloli wadanda babu su a zahiri, rarrabe kwangiloli da kuma rashin mutunta dokar bada kwangilar.

Majalisar wakilai za ta binciki 'batan dabo' da N100bn ta yi ta inganta arewa maso gabas
Majalisar wakilai za ta binciki 'batan dabo' da N100bn ta yi ta inganta arewa maso gabas. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kurunkus: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana 'yan majalisar da suka karbe kwangilar NDDC

"Akwai zargi da ke nuna cewa ministan jin kai, tallafi da walwalar 'yan kasa, Sadiya Farouk, ta shiga wannan harkallar da manajan daraktan hukumar. Suna cire makuden kudi don siyan motocin yaki ba tare da izinin hukumar ba.

"Wannan abu kuwa ya take dokar kasar nan kuma dole a tsawatar a kai," ya kara da cewa.

Majalisar ta amince da wannan bukatar bayan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya aiwatar da zabe.

An mika bukatar ga kwamitin kudi na hukumar kula da ci gaban yankin arewa maso gabas. Ana tsammanin samun rahoton binciken a nan da makonni takwas.

Wannan ci gaban ya bayyana ne bayan da majalisar ta kammala bincike a kan almundahanar kudi har N81.5 biliyan da hukumar kula da habaka yankin Neja Delta tayi.

Har a yanzu dai ba a kammala fitar da rahoton binciken ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel