'Yan bindiga sun saki fursunoni a Barikin Ladi

'Yan bindiga sun saki fursunoni a Barikin Ladi

Rahotannin da ke shigowa a yanzu sun tabbatar da cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari kan jami'an tsaron gidan yari a Barikin Ladi, sun aikata mummunar ta'asa.

Kafar watsa labarai ta TVC news ta ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hari kan jami'an tsaron gidan kurkuku a Barikin Ladi da ke jihar Filato, inda suka saki fursunoni.

'Yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne, sun kai hari kan ayarin jami'an hukumar gidajen gyara hali a kusa da Babbar Kotun Filato da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi, inda suka 'yantar da masu laifi shida.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, harin na kwanton bauna ya auku ne a yayin da ake jigilar wasu mutane 14 da ake zargi da laifuka daban-daban kama daga kisan kai, garkuwa da mutane da kuma fyade.

'Yan bindiga sun saki fursunoni a Barikin Ladi
'Yan bindiga sun saki fursunoni a Barikin Ladi
Asali: Facebook

Wani mutum da shaidi aukuwar wannan lamari, ya ce ayarin bayan isowarsa harabar Kotun, 'yan bindigar da suka noke a bakin Kotun, suka bude wuta tare da sakin fursunoni ba tare da an iya mayar musu da martani ba.

Kwamandan hukumar tsaron gidajen kaso na jihar Filato, Mista S. A Musa, ya ce kotun ba ta sanarwa da kwamishinan 'yan sandan jihar ba, Edward Egbuka, cewa an sauya ranar sauraron karar masu laifin.

Sai dai jami'an 'yan sanda sun samu nasarar cafke wasu mutum da ke zargi da aikata wannan laifi.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta cigaba da samun gagarumar nasara a kokarin da take yi na kawo karshen aiyukan 'yan bindiga da ke satar shanu, garkuwa da mutane, da sauran miyagun laifuka.

A ranar 18 ga watan Yuli ne dakarun rundunar soji suka kama wasu 'yan bindiga biyu; Marti Abdullahi da Abdullahi Muazu, a kauyen Gundumi da ke karamar hukumar Isah a jihar Sokoto.

A cikin wata sanarwa da rundunar soji a yau, Alhamis, ta ce ta kama 'yan bindigar bayan samun sahihan bayanai a kan al'amuransu.

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun rundunar soji sun sake kama wasu gagararrun 'yan bindiga biyu; Gabbe Muhammad da Muhammad Bello, a kauyen Mai Filoti da ke yankin karamar Sabon birni a jihar Sokoto.

KARANTA KUMA: Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Neja ya yi murabus

Gaabbe da Bello sun kasance sanannu a bangaren garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, kamar yadda rundunar soji ta bayyana.

Kazalika, dakarun rundunar soji da ke aiki a jihar Katsina sun samu nasarar kama wasu 'yan bindiga biyu; Mohammed Lawal da Useni Abubakar, a kauyen Nahuta da ke karamar hukumar Batsari.

Mazauna Nahuta sun sanar da rundunar soji cewa masu 'yan bindigar sun jagoranci kai hare - hare kauyukan a lokuta daban - daban.

Rundunar soji ta kara da cewa dakarunta sun kara kama wani dan bindiga a kauyen Yar Tasha tare da bayyana cewa yanzu haka ana neman sauran abokansa da suka kirashi a waya bayan ya shiga hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel