Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Neja ya yi murabus

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Neja ya yi murabus

Mun samu rahoton cewa, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Nijar, Honarabul Bako Kasim Alfa ya yi murabus haka siddan.

Ya sanar da sauka daga kujerarsa ne a yayin zaman majalisar dokokin jihar da ake gudanarwa a yau Alhamis, 23 ga watan Yuli.

Sanarwar sauka daga kujerarsa tana kunshe ne a cikin wata wasika da aka gabatar wa shugaban majalisar kuma aka karanta a zauren majalisar.

Sai kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, mataimakin kakakin majalisar bai fayyace dalilin da ya sa ya yi murabus ba.

Majalisar Dokokin jihar Neja
Hoto daga jaridar The Nation
Majalisar Dokokin jihar Neja Hoto daga jaridar The Nation
Asali: Twitter

Babu wata-wata dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Paikoro, Suleiman Gambo Aninigi, ya gabatar da kudirin a maye gurbin mataimakin kakakin majalisar.

Cikin gaggawa dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Kontagora, Sale Ibrahim Alhaji, ya goyi bayan kudirin.

KARANTA KUMA: A karon farko Buhari ya sanya takunkumin rufe fuska yayin tafiyarsa zuwa kasar Mali

A yanzu sabon mataimakin kakakin majalisar shi ne Jibrin Ndagi Baba, dan majalisa mai wakilcin karamar hukumar Lavun.

A wani rahoton da Legit.ng ta ruwaito, Ma'aikatar kwadago da aikin yi ta ce karamin ministanta, Festus Keyamo ne zai jagoranci daukar ma'aikata 774,000 a karkashin shirin ma'aikatar ta musamman.

Ma'aikatar ta sanar da hakan ne a martanin da tayi a kan bukatar majalisar tarayya na cewa a dakatar da ministan daga shugabantar daukar aikin.

Majalisar dattawan ta ce a maimakon ministan, a bai wa hukumar samar da aikin yi NDE damar jagorantar al'amarin.

Keyamo a baya bayan nan ya yi musayar yawu da wasu 'yan majalisar a yayin da ya bayyana gaban kwamitinsu don bayani a kan shirin.

'Yan majalisar sun zargi Keyamo da yi kane-kane kan shirin a maimakon mika shi ga hukumar NDE, amma ministan ya yi martani da cewa 'yan majalisar na kokarin yiwa lamarin hawan kawara don a basu wasu gurabe na aikin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng