Kurunkus: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana 'yan majalisar da suka karbe kwangilar NDDC

Kurunkus: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana 'yan majalisar da suka karbe kwangilar NDDC

Ministan kula da harkokin yankin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya ce ba yana nufin 'yan majalisar bane aka bai wa kwangilolin hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta.

Akapbio ya sanar da hakan ne a wata wasikar martani da ya mika ga kakakin majalisar wakilan a ranar Alhamis, Premium Times ta wallafa.

A ranar Talata, majalisar ta bai wa Akpabio sa'o'i 48 a kan ya wallafa sunayen 'yan majalisar tarayyar da ya zarga cewa sun mora daga kwangilolin NDDC.

Wannan kirar kakakin majalisar ya zo ne bayan da Akpabio ya bayyana cewa kusan kwangilolin da aka fitar na NDDC sun tafi ne ga 'yan majalisar tarayyar. Ya sanar da hakan ne yayin da ake tuhumarsa a gaban kwamitin kula da harkokin yankin.

Wannan fallasar ta ruda zauren majalisar har zuwa lokacin da mukaddashin shugaban kwamitin, Thomas Ereyitomi, ya tsawatar wa da 'yan majalisar.

Wasikar Akpabio ta iso ne yayin da aka yi rabin zaman majalisar yayin da kakakin ya bayyana niyyarsa ta maka shi a kotu a kan zargin bacin suna.

A wasikar Akpabio, ya janye kalamansa inda ya ce da yawa daga cikin 'yan majalisar da ta gabata ne suka karbar kwangilolin.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel