'Yan sanda sun damke yara masu shekaru 13 zuwa 17 suna fim din batsa

'Yan sanda sun damke yara masu shekaru 13 zuwa 17 suna fim din batsa

'Yan sanda sun damke wasu matasa 25, mata 10 da maza 15, a yayin da ake zargin su da yin bidiyon batsa a yankin Kakamega da ke kasar Kenya.

Matasan da suka raba kansu biyu-biyu da uku-uku na da shekaru 13 zuwa 17. Shugaban wadanda ake zargin kuma mashiryin fim din sunansa Caleb.

Wani ganau ba jiyau ba mai sana'ar kwashe bola, ya ce hankalinsa ya kai kansu ne yayin da ya tsinta Leda baka cike da kwaroron roba. Ya ga matasan na lalata yayin da wani ke nada a bidiyo. Tuni ya kira jami'an 'yan sanda.

Ganau ba jiyau ba ya ce; "Ina aikina na kwashe shara ne na ga wani abun mamaki. Na samu kwaroron roba masu yawa a bakar leda sannan na ji hayaniya daga wani gida.

"A lokacin da na shiga gidan, na sha matukar mamaki domin kuwa mata na ga suna lalata kuma wani mutum yana nada.

"A take na sanar da 'yan sanda kuma da gaggawa suka iso inda suka kama wadanda ake zargin. Sun yi lalata da kwaroron roba yayin da wasu suka yi babu shi."

OCPD na yankin Kakamega, David Kabena ya tabbatar da kamen.

"Duk wadannan kananan yara da muka kama suna lalata za mu ladabtar da su. Za mu tsananta horo ga Caleb don shine yake batar da su," cewarsa.

KU KARANTA: Da duminsa: Boko Haram ta saki bidiyon kisan gilla da suka yi wa ma'aikatan SEMA da mai gadi

An kama matasa 25 yayin da suke yin fim na batsa
An kama matasa 25 yayin da suke yin fim na batsa. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

A wani labari na daban, wani mutum mai shekaru 40 mai suna Edet Imoh, ya amsa laifin da ake zarginsa a gaban 'yan sandan jihar Legas.

Ya tabbatar da cewa yayi lalata da diyar makwabcinsa mai shekaru 11 "amma sau shida kacal ba kamar yadda mahaifiyar yarinyar ke cewa da yawa ba".

'Yan sanda sun kama Imoh wanda ke zaune a titi daya da mahaifan yarinyar a titin Oyekanle da ke Bariga da ke tsakiyar birnin Legas, bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai wa ofishin 'yan sanda da ke Bariga a ranar 25 ga watan Yunin 2020.

An zargi cewa, a duk lokacin da wanda ake zargin ke son lalata da yarinyar, zai kirata dakinsa a kan cewa zai aiketa siyo wani abu. Asiri ya tonu bayan da wani makwabcinsu ya lura da hakan tare da sanar da mahaifiyar yarinyar yayin da take neman diyarta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya ce "an kama wanda ake zargi wando a kasa yayin da karamar yarinyar ke kwance yana lalata da ita.

"A yayin da aka tambayeshi yayi bayanin abinda ya faru sai yace aikin shaidan ne. Ya ce sau shida kacal ya taba lalata da yarinyar ba sau da yawa ba da mahaifiyarta ke ikirari."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel