Boko Haram: Buhari ya yi Allah wadai da kashe ma'aikatan SEMA guda 5 a Borno

Boko Haram: Buhari ya yi Allah wadai da kashe ma'aikatan SEMA guda 5 a Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan gillar da mayakan Boko Haram sukayiwa ma'aikatan hukumar bada agajin gaggawa SEMA guda biyar a jihar Borno. Kusan wata daya ke nan da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da ma'aikatan.

Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba ta hannun Garba Shehu, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan ma'aikatan da suka ransu.

Shugaban kasar, wanda ya roki Allah ya ba iyalan juriyar wannan babban rashi da suka yi, ya kuma tabbatarwa iyalan cewa gwamnatinsa zata ci gaba da yin duk mai yiyuwa don ganin ta kawo karshen Boko Haram.

Shugaba Buhari ya kuma jajantawa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA, wadanda mummunar waki'ar ta fada kansu.

Buhari, ya gode masu akan jajircewar da suke yi kullum wajen kai tallafi ga wadanda harin Boko Haram ya shafa a Arewa maso Gabas.

Ya kuma basu tabbacin cewa jami'an tsaro zasu ci gaba da aiki da hukumar kafada da kafada domin ganin cewa irin hakan bata sake faruwa ba.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince da rabawa matasa tallafin jari na naira biliyan 75

Boko Haram: Buhari ya yi Allah wadai da kashe ma'aikatan SEMA guda 5 a Borno
Boko Haram: Buhari ya yi Allah wadai da kashe ma'aikatan SEMA guda 5 a Borno
Asali: Twitter

A wani labarin makamancin wannan, Majalisar zartaswa ta kasa (FEC) ta amince da ware N75bn domin samar da shiri na musamman da zai tallafawa matasan kasar, da nufin bunkasa rayuwarsu.

Ministan matasa da waanni, Sunday Dare ya bayyana hakan ga 'yan jaridun fadar shugaban kasa, bayan fitowa daga taron majalisar zartaswar da aka shafe awanni takwas ana yinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman majalisar zartaswar.

A cewarsa, wadanda ke a cikin shekarun samartaka kuma masu tsarin kasuwanci na gaskiya kuma suke zaune a kusa da inda aka gina bankunan 'yan kasuwa 125 a fadin kasar, kuma suka cancanta ne kawai zasu ci gajiyar tallafin.

Dare ya bata tabbacin cewa kamar yadda akayi shirin N-Power, haka shima wannan zai kasance komai a na'ura kuma za a takaita akan masu shekaru 18 zuwa 35.

Ya jaddada cewa ba za a duba banbanci addini, yare ko tsarin rayuwa wajen bayar da tallafin ba, duk wanda ya cancanta zai ci gajiyar tallafin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel