Buhari ya amince da rabawa matasa tallafin jari na naira biliyan 75

Buhari ya amince da rabawa matasa tallafin jari na naira biliyan 75

- Majalisar zartaswa ta amince da rabawa matasan Nigeria tallafin N75bn domin bunkasa rayuwarsu

- An takaita wadanda zasu ci gajiyar shirin daga masu shekaru 18 zuwa 35, kuma ba za a duba banbanci addini ko yare ko muhallin zama ba

- Ya zama dole wadanda zasu ci gajiyar shirin ya zamo suna da kyakkyawan tsari na kasuwanci kuma sun tsallake tantancewa

Majalisar zartaswa ta kasa (FEC) ta amince da ware N75bn domin samar da shiri na musamman da zai tallafawa matasan kasar, da nufin bunkasa rayuwarsu.

Ministan matasa da waanni, Sunday Dare ya bayyana hakan ga 'yan jaridun fadar shugaban kasa, bayan fitowa daga taron majalisar zartaswar da aka shafe awanni takwas ana yinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman majalisar zartaswar.

A cewarsa, wadanda ke a cikin shekarun samartaka kuma masu tsarin kasuwanci na gaskiya kuma suke zaune a kusa da inda aka gina bankunan 'yan kasuwa 125 a fadin kasar, kuma suka cancanta ne kawai zasu ci gajiyar tallafin.

Dare ya bata tabbacin cewa kamar yadda akayi shirin N-Power, haka shima wannan zai kasance komai a na'ura kuma za a takaita akan masu shekaru 18 zuwa 35.

Ya jaddada cewa ba za a duba banbanci addini, yare ko tsarin rayuwa wajen bayar da tallafin ba, duk wanda ya cancanta zai ci gajiyar tallafin.

KARANTA WANNAN: Wutar lantarki ta haddasa gobara a Ofishin NTA na Ilorin, dakuna 3 da dakin taro sun kone

Buhari ya amince da rabawa matasa tallafin jari na naira biliyan 75
Buhari ya amince da rabawa matasa tallafin jari na naira biliyan 75
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa gobara ta tashi a daren ranar Talata a ginin ofishin talabijin na NTA, da ke Ilorin, jihar Kwara.

Gobarar, wacce ake da yakinin wutar lantarki ce ta haddasa ta, ta fara ne da misalin karfe 11:25 na daren kuma ta shafi dakuna uku da dakin taro.

Mai magana da yawun hukumar 'yan kwana kwana na jihar Kwara Hassan Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar The Nation.

Ya ce: "Daga cikin ofisoshi 28 na cikin ginin, ofisoshi uku ne kawai suka kone da kuma dakin taro." Adekunle ya ce 'yan kwana kwana

"sun isa ginin da misalin karfe 11:29 mintuna hudu bayan da aka rufe watsa labarai na wannan rana.

"Duk da cewa lokacin da suka isa wajen, wutar na ci sosai kuma har ta mamaye wurare da dama a cikin ginin

"Yan kwana kwanan sun samu nasarar kashe wutar ta hanyar amfani da kayan aikinsu na zamani."

Ya bukaci "daukacin al'umma (musamman masu aiki) da su kasance suna kashe dukkanin kayayyakin wutar lantarki bayan tashi daga aiki."

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar ya jajantawa hukumar gudanar NTA kan faruwar wannan lamari.

A cikin wata sanarwa daga bakin mai magana da yawunsa, Rafiu Ajakaye, gwamnan ya ce ya isa ginin gidan talabijin din da misalin karfe daya na ranar Laraba.

Ya ce lallai da gobarar ta lashe dukkanin ginin amma sakamakon hadin karfi tsakanin 'yan kwana kwana na gwamnatin tarayya da na jiha, an shawo kanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel