Guguwar Buhari ba zata yima aiki a 2023 ba, APC ta gargadi mambobinta

Guguwar Buhari ba zata yima aiki a 2023 ba, APC ta gargadi mambobinta

- APC ta gargadi mambobin jam'iyyarta da kada su kuskura su sanya a ransu wai tasirin Buhari zai taimaki jam'iyyar a zaben 2023

- Jam'iyyar tace ma damar tana son ci gaba da mulki har bayan 2023 to dole sai ta fara yakin zabe daga matakin farko

- Ta kuma yanke shawarar yin bikon mambobin jam'iyyar da suka samu sabani domin ta dawo tsintsiya madaurinki daya

Jam'iyyar APC ta ce kada wani dan takara ko mai neman takara a babban zaben 2023 a karkashin jam'iyyar ya kuskura ya ce zai dogara da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin cin zabe.

Jam'iyyar ta ce fara yakin zabe tun daga matakin farko, da kuma karfafa shiga lunguna da sako don yakin zabe zai taimakawa jam'iyyar wajen ci gaba da shugabantar kasar.

Wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ci zabensa na farko a APC a 2015 kuma ya sake cin zaben 2019 zai zo karshe a shekarar 2023, inda za a gudanar da wani zaben.

Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar reshen tarayya, Sanata John Udoedge, ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin hadakar kunfiyoyin magoya bayan APC karkashin jagorancin Mr Frank Ossai, a sakatariyar jam'iyyar a ranar Laraba.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince da rabawa matasa tallafin jari na naira biliyan 75

Sanata John Udoedge ya bayyana cewa kungiyoyin da ke nuna goyon baya ga jam'iyyar sune suka taimaka har jam'iyyar ta kai matsayin da take a yanzu.

Guguwar Buhari ba zata yima aiki a 2023 ba, APC ta gargadi mambobinta
Guguwar Buhari ba zata yima aiki a 2023 ba, APC ta gargadi mambobinta
Asali: UGC

Ya ce jam'iyyar ta cimma matsyar yin sulhu tsakaninta da mambobinta da suke fushi da jam'iyyar, domin ganin jam'iyyar ta zamo tsintsiya madaurinki daya.

Udoedghe y shawarci mambobin kungiyoyin magoya bayan jam'iyyar da su cusa kansu a yakin zabe tun daga matakin farko, domin kuwa shaharar Buhari ba zata taimakawa jam'iyyar a zaben 2023 ba.

"A 2023, shahara da tasirin shugaba Buhari ba zai yi mana aiki ba. Don haka muna da bukatarku kungiyoyin magoya baya a wannan tafiyar. Dole muyi wani abu akan hakan.

"Duba da muhimmancinku a cikin jam'iyyar, mun yanke shawarar yin bikon duk wani mamba da muka samu sabani da shi domin tabbatar da cewa jam'iyyar ta tsaya da karfinta," a cewarsa.

Udoedghe ya kara da cewa kwamitin rikon kwarya na shugabancin jam'iyyar a matakin kasa karkashin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni zata magance matsalolin jam'iyyar.

Tun farko, Ossai, wanda mambobinsa aka batawa rai kan waresu da akeyi a ayyukan jam'iyyar APC, ya bukaci jam'iyyar data sakawa mambobinta ta hanyar sanyansu a gudanar yakin zaben gwamnonin jihohin Edo da Ondo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel