An sako ɗiyar ɗan majalisar da aka yi garkuwa da ita a Kano

An sako ɗiyar ɗan majalisar da aka yi garkuwa da ita a Kano

Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, ɗiyar ɗan majalisar da aka yi garkuwa da ita a Kano, Juwairiyya Murtala, ta kuɓuta daga hannun masu ta'adar garkuwa da mutane.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Juwairiyya ta koma gidan mahaifinta da ke Unguwar Kore a karamar hukumar Dambatta da misalin uku na ranar Talata da daddare.

Wani ɗan uwan Juwairiyya, Nura Yusha'u Kore, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai da cewa ta dawo gida cikin koshin lafiya.

A ranar Asabar da din da ta gabat ne masu garkuwa da mutane suka sace 'yar gidan ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Dambatta, Alhaji Murtala Musa Kore.

Masu ta'adar garkuwar sun yi awon gaba da budurwar mai shekaru 17 a duniya yayin da suka yi yunkurin yin garkuwa da mahaifinta wanda ba su riska ba a gida.

Juwairiyya Murtala Kore
Hoto daga Freedom Radio
Juwairiyya Murtala Kore Hoto daga Freedom Radio
Asali: Twitter

Don haka suka tasa ƙeyar Juwairiyya wadda ɗalibar aji biyar ce a makarantar Sakandire ta GSS Jogana kuma ita ce 'yar auta a wurin mahaifinta kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Ana dai ci gaba da samun matsalar garkuwa da mutane a Najeriya musamman jihohin arewa maso yamma.

Babu shakka a baya bayan nan an ci gab da fuskantar matsalar garkuwa da mutane a kasar musamman a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta damke wani mutum mai shekaru 39 mai suna Obiora Patrick sakamakon zarginsa da ake da lalata diyar matarsa.

KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun sace sarki a Nasarawa, suna neman fansar N7m

A takardar da ta fita daga hannun kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da yarinyar ke asibiti.

DSP Nguroje ya yi kira ga jama'a da su bada goyon baya wurin yaki da cin zarafin da sauran laifuka masu alaka ga hakan. Ya yi kira ga iyaye da su dinga bada kulawa ga 'ya'yansu.

Ya ce, "Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa tana sanar da jama'ar cewa za ta tsananta bada kariya ga mata da kananan yara.

"A ranar 20 ga watan Yulin 2020, ta damke wani mutum mai suna Obora Patrick mai shekaru 39 a Jimeta da ke karamar hukumar Yola ta arewa a kan lalata da diyar matarsa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel