‘Yan bindiga sun sace sarki a Nasarawa, suna neman fansar N7m

‘Yan bindiga sun sace sarki a Nasarawa, suna neman fansar N7m

'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake a jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad Dankawo.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Dankawo shi ne mai rawanin Ardo Udege a karamar hukumar Udege ta jihar Nasawa wanda 'yan bindiga suka yi awon gaba da shi a fadarsa.

An tattaro cewa, wadanda suka yi garkuwa da Dankawo sun nemi kudin fansa na naira miliyan bakwai domin sakinsa.

Shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad Hussaini, shi ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata.

Alhaji Husssini ya shaidawa manema labarai cewa a watan Yuni kadai, masu garkuwa da mutane sun kashe akalla Fulani makiyaya 6 tare da sace musu shanu fiye da 300.

Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya; Muhammadu Adamu
Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya; Muhammadu Adamu
Asali: Facebook

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wasu 'yan bindiga sun dira karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja tare da yin awon gaba da mutane 16 a kauyukan Magami da Tungan-Bako.

Rahotanni kamar yadda manema labarai na jaridar The Nation suka tabbatar ya nuna cewa, 'yan bindigar sun dira kauyen a kan baura tare da fara yin harbin 'kan mai uwa da wabi'.

A cewar rahoton jaridar, 'yan bindigar sun yi awon gaba da mutane 8 a kauyen Magami tare da sake tafiya da wasu mutum 6 a kauyen Tungan Bako.

KARANTA KUMA: Gwamnati kadai ba za ta iya inganta gine-ginen kananan makarantu ba - Nwajiuba

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa, 'yan bindigar sun shiga gida - gida, inda suke fito da mutane tare da kwace musu kayayyakinsu masu muhimmanci.

Ibrahim Inga, babban darektan hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) reshen jihar Neja, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari

Sai dai Inga bai bayar da wani karin bayani ba bayan tabbatar da cewa an kai harin da safiyar ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel