Ondo 2020: Yadda Akeredolu ya lashe tikitin takara na jam'iyyar APC

Ondo 2020: Yadda Akeredolu ya lashe tikitin takara na jam'iyyar APC

Gwamnan da ke kan karagar mulki a jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya sake lashe tikitin takarar gwamnan jihar a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Akeredolu shine zai kasance marikin tutar jam’iyyar mai mulki a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba na bana.

Wakilai sama da 3,000 ne suka kada kuri'unsu a zaben wanda aka shafe sama da awanni shida ana gudanarwa tun daga karfe 2.00 na rana har zuwa 8:30 na Yamma a ranar Litinin.

An kammala tantancewa da kidayar kuri'u da misalin karfe 11:20 na dare kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Akeredolu yayi nasara a dukkanin kananan hukumomin jihar, inda ya samu kuri'u 2,458. Ya tika sauran manema takara bakwai da kasa.

Rotimi Akeredolu
Rotimi Akeredolu
Asali: Twitter

Wanda ya biyo bayansa a mataki na biyu, Olusola Oke, kuri'u 262 kacal ya samu yayin da Isaac Kekemeke da ya zo a na uku ya tashi da kuri'u 19.

Sauran manema takara da da kowannensu ya samu kur'i'u kasa da goma sun hadar da; Olayide Adelami, Jumoke Anifowose, Sola Iji, Awodeyi Akinsehinwa da Bukola Adetula.

Wasu daga cikin manema takarar da suka janyewa Akeredolu takara tun gabanin zaben sun hadar da; lfe Oyedele, Olusegun Abraham, Jimi Odimayo da Nathaniel Adojutelegan.

KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Ya kamata Masari ya yi murabus shi da duk 'yan majalisarsa - Mahdi

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi wanda ya sanar da sakamakon zaben, ya ce tabbas wannan nasara da Akeredolu ya yi manuniya ce ta soyayyar da mambobin jam'iyyar APC na jihar ke masa.

Gwamna Bello ya nemi sauran manema takarar da suka sha kasa a kan su goyi bayan Gwamna Akeredolu domin wanzuwar jam'iyyarsu ta APC kan kujerar mulki a jihar.

Ga adadin kuri'un da kowane manemin tikitin takara ya samu yayin zaben na fidda gwani:

Olaiye Adelami: 4

Bukola Adetula: 0

Nathaniel Adojutelegan: 4

Jumoke Anifowose: 2

Rotimi Akeredolu: 2,458

Awodeyi Akinsehinwa: 4

Sola lji: 9

Isaac Kekemeke: 19

Jimi Odimayo: 0

Ife Oyedele: 1

Sola Oke: 262

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel