Rashin Tsaro: Ya kamata Masari ya yi murabus shi da duk 'yan majalisarsa - Mahdi

Rashin Tsaro: Ya kamata Masari ya yi murabus shi da duk 'yan majalisarsa - Mahdi

Shehu Mahadi ya ce ya kamata tuni gwamna Aminu Masari ya dade da yin murabus tare da duk 'yan majalisarsa sakamakon tashe-tashen hankula da rashin tsaro da ya mamaye jihar Katsina.

Furucin Mahadi wanda gogarman dan kasuwa ne a jihar Kaduna, ya zo a yayin da yake zantawa da manema labarai na Gidan Talbijin din Channelsa a wani shiri na Sunrise Daily.

Mahadi wanda mutum ne mai fafutikar kare hakkin dan Adam, ya ce gwamnatin Katsina ta gaza tsare rayuka da dukiyar al'umma ballantana kuma ta iya tsare musu mutuncinsu da martaba.

Don haka yake cewa tun-tuni ya dace Gwamna Masari da shi da makarrabansa su yi murabus domin sun gaza sauke jigo cikin nauye-nauyen da suka rataya a wuyansu.

Yana cewa: "Duk wanda ya fito ya yi ikirarin yana iyaka bakin kokarinsa, to kuwa kokarin da yake ba ya da wani tasiri."

Gwamnan Katsina da wasu manyan jiha
Gwamnan Katsina da wasu manyan jiha
Asali: Facebook

"Nan ba dadewa Gwamna, Mai Martaba , kuma dan uwana Aminu Bello Masari, ya fito fili ya bayayana cewa ba zai iya kallon al'ummar jihar Katsina da idanunsa ba domin kuwa kunya ba za ta bar shi ba."

"Masari ya ce kunya ba za ta bari ya iya yin ido hudu da al'ummar jihar Katsina ba domin kuwa ya gaza basu kariya."

"Babi na 2 na kundin tsarin mulki ya fayyace mana karara abin da ya sa mutane ke shiga shugabanci kuma me ya janyo samuwar gwamnatin tunda farko; shine don kare rayuka, dukiya da mutuncin al'umma."

"Amma a yayin da ake kashe mutane kamar beraye kuna ana kone musu gidaje da kadarori gami da yi wa mata fyade, ina kuma maganar kare musu mutunci?"

KARANTA KUMA: Kudin tsaro: Mahadi Shehu ya zargi Gwamnatin Katsina da batar da N24.b a iska

"Wannan shine mafi girman dalilin da yasa ya kamata ya yi murabus tare da duk 'yan majalisarsa, domin kuwa ya tabbatar da cewa ya gaza a kujerar mulki."

"Kuma wannan yana faruwa ne duk da cewa gwamnatin Katsina a tsakanin watan Yunin 2015 zuwa Yunin 2020 ta kashe Naira biliyan 52 da sunan tsaro, amma duk da haka rashin tsaro yana karuwa."

"Wannan shi yake nuna cewa yawan kudin da ake kashewa shine yawan mutanen da ake kara kashewa da yawan mutanen da ake hana wa tsugunno a muhallansu," inji Mahdi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel