Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Aso Rock

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Aso Rock

- Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa karo na tara ana kiyaye dokar nesa-nesa da juna

- Ministoci 7 sun halarci zaman majalisar da shugaba Buhari ya jagoranta a yau Laraba, 22 ga watan Yuli

- Yayin zaman majalisar, an yi alhinin mutuwar aminin Buhari, Mallam Isma'il Isa Funtua

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja.

Wannan shine zaman majalisar na tara da shugaban kasar yake jagoranta ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

Zaman majalisar ya fara gudana da misalin karfe 10.00 na safiyar Laraba, 22 ga watan Yuli.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, 'yan majalisar kalilan ne suka hallara a zauren da ake gudanar da taron, yayin da dama suke halartarsa ta hanyar bidiyo da aka hada ta yanar gizo.

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Aso Rock
Hoto daga fadar shugaban kasa @Buharisallau1
Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Aso Rock Hoto daga fadar shugaban kasa @Buharisallau1
Asali: Twitter

Kusoshin gwamnatin da suka halarci zaman a wannan mako sun hadar da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Haka zalika shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi Esan, ta halarci zaman majalisar tare da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno.

Ministocin da a dole su na da ta cewa kuma su na dauke da bayanan da za su gabatar su ne kadai suka halarci zaman majalisar a fadar shugaban kasa.

Ministoci 7 ne suka halarci zaman ciki har da; Ministan kudi kasafi da tsare-tsaren - Zainab Ahmed; Ministan Sufuri - Honarabul Rotimi Amaechi; Ministan Labarai da Al'adu - Alhaji Lai Mohammed.

KARANTA KUMA: Ma'aikata 774,000: Sanata ya yiwa Keyamo barazana da shiga gidan yari

Sauran sun hadar da; Ministan Ayyuka da Gidaje - Babatunde Fashola; Ministan Shari'a Kuma Lauyan Koli na Kasa - Abubakar Malami; Ministan Harkokin Cikin Gida - Ogbeni Rauf Aregbesola.

Sai kuma Ministan Matasa da Wasanni - Sunday Dare da kuma Karamin Ministan Ilimi - Chukwuemeka Nwajiuba.

Bayan rera taken Najeriya a zaman majalisar na yau, Sakataren Gwamnatin ya nemi da a yi shiru na minti daya domin yin alhinin mutuwar Mallam Isma'il Isa Funtua da ajali ya katse masa hanzari a ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel