Ta fasu: An gano yunkurin handame N22m na tallafin bankin duniya a Kano

Ta fasu: An gano yunkurin handame N22m na tallafin bankin duniya a Kano

Wata kungiyar masu kishin kasa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano, ta mika korafi a kan sakataren ilimi na karamar hukumar, Ado Abdu-Kwa, a gaban hukumar kula da rashawa da laifuka majibantansa mai zaman kanta (ICPC).

Ana zarginsa da yunkurin waskar da wasu kudi har N22,140,000 da bankin duniya ya bada don tallafi ga ilimi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, bankin duniya tare da hadin guiwar Global Partnership for Education, wadanda suka kware wurin bada tallafi ga yankunan da ke da matsala a bangaren ilimi, sun zabi jihar Kano a cikin jihohin arewa maso yamma don bada tallafi.

An gano cewa kananan hukumomi 11 da suka hada da Dawakin Tofa a jihar Kano ne za su mori tallafin. An zabi makarantun firamare 100 inda za a fara da 58 a kashin farko.

An gano cewa shugaban GPE na kasar, ya bada N383,000 ga kowacce makaranta 58 da ke karamar hukumar a matsayin tallafi.

An tura kudaden a asusun bankin makarantun inda shugaban kwamitin gudanarwa na makaranta da shugabannin makarantun za su zama masu iya fitar da kudin.

Kamar yadda dokar tallafin GPE ta bayyana, za a yi amfani da wadannan kudin don tabbatar da manyan ayyuka a makarantun.

Wasu majiyoyi masu karfi sun tabbatar wa Daily Nigerian cewa ,duk an samu al'amuran makamantan hakan wurin waskar da kudaden da bankin duniyar ta bada na tallafi a kananan hukumomi 10 na jihar.

A korafin da kungiyar ta fitar mai kwanan wata 20 ga Yulin 2020, kungiyar ta zargi Abdu-Kwa da yin taro a ranar 13 ga watan Yulin 2020 inda ya umarci shugabannin makarantun 58 da su tura kudin tallafin zuwa asusun bankinsa.

Kamar yadda korafin da ya samu sa hannun Muhammad Sanusi Danyaya ya bayyana, kungiyar ta zargi ES da sake yin wani taron a ranar 14 ga watan Yuli inda ya sake maimaita wannan umarnin.

Kungiyar ta zargi cewa, a lokacin da shugabannin makarantun suka ki yin biyayya, ya ce wannan umarni ne daga kwamishinan ilimi na jihar Kano don tabbatar da cewa sun tura wadannan kudaden a asusun banki daya.

Ta fasu: An gano yunkurin handame N22m na tallafin bankin duniya a Kano
Ta fasu: An gano yunkurin handame N22m na tallafin bankin duniya a Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamna a arewa ya dakatar da basarake a jiharsa

A korafin, kungiyar ta ce shugabannin makarantun sun ki yi biyayya inda suka ce dokar tallafin ita ce, yankuna za su iya fadin yadda suke so a kashe musu kudin kuma a nuna yadda aka kashe kudin.

"A kokarin tabbatar da an waskar da kudin, sakataren ilimi Ado Abdu-Kwa, ya sake gayyatar shugabannin makarantun wani taro a ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2020 wurin karfe 10 na safe.

"Ya yi musu barazanar cewa kada su kuskura su kai ranar Juma'a, 25 ga watan Yuli basu turo kudin ba. Don kuwa dukkan sauran kananan hukumomi 10 suna bada hadin kai.

"Shugabannin makarantun sun jaddada cewa basu iya cire ko kwabo ba tare da sa hannun shugaban SBMC ba saboda asusun bankin na hadin guiwa ne," kungiyar ta zarga.

A kokarin sakataren ilimin na jan hankulan shugabannin makarantun da SBMC, ya ce su turo N350,000 sai su raba N33,000 a tsakaninsu.

A yayin da aka tuntubi kwamishinan ilimi, Sunusi Kiru, ya fara musantawa a kan sanin komai game da lamarin tare da cewa a tuntubi Abdu-Kwa.

Duk wani kokari na tuntubar sakataren ilimin ya gagara saboda lambar wayarsa bata shiga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel