Da duminsa: Gwamnatin Jigawa ta soke bukukuwan babbar Sallah

Da duminsa: Gwamnatin Jigawa ta soke bukukuwan babbar Sallah

Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya soke bukukuwan babbar Sallar Lahya a jihar da kuma dakatar da sarakuna biyar masu daraja na jihar daga jagorantar duk wani hawan Sallah ko hawan daushe a babbar Sallar wannan shekarar.

Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

A tattaunawar, ya ce wannan umurnin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na ci gaba da yaki don dakile yaduwar cutar COVID-19.

Ya bayyana cewa, jihar a yanzu ta samu gagarumar nasara ta wannan fuskar, kasancewar bata samu bullar cutar ba kusan kwanaki 30 yanzu.

Gwamnan jihar ya bayyana cewa: "duk da irin wannan nasarar, dole ne jihar ta bi duk wasu matakai na dakile bullar cutar da kuma daukar matakan kariya na dakile yaduwarta."

A cewarsa, "Manyan motoci 110 cikin 150 makare da kayan abinci sun iso cikin jihar kuma an turasu zuwa ga al'umomin da zasu ci gajiyar tallafin."

Ya jaddada cewa za ayi rabon kayan abincin ne a gundumomi 287 da ke a kananan hukumomi 27 da ke jihar. "Zamu tabbata kowa ya samu wannan tallafi domin za abi tsari mai kyau."

Ya ce a wannan lokacin, "har yanzu mutum daya ne kawai ya rage a cibiyar killace masu dauke da cutar. An rufe cibiyon Fanisau da Birninkudu, amma suna a tsaftace don jiran ko ta kwana.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Mutane 562 sun sake kamuwa da cutar COVID-19 a Nigeria

Da duminsa: Gwamnatin Jigawa ta soke bukukuwan babbar Sallah
Da duminsa: Gwamnatin Jigawa ta soke bukukuwan babbar Sallah
Asali: Depositphotos

Badaru ya kara bayyana cewa tuni 'yan kasuwa suka bi matakan kariya musamman na bada tazara, shi yasa aka bude kasuwannin tun farko.

Sai dai gwamnan ya bukaci daukacin al'ummar jihar da su ci gaba da kara hakuri, a yayin da jihar ke kokarin samar da karin tallafin kayan abincin.

A wani labari kuwa, alkalumman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC), ya bayyana na ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2020, sabbin mutum 562 sun sake kamuwa da korona a Najeriya.

Ga bayani daki-daki, jiha bayan jiha.

FCT-102

Lagos-100

Plateau-52

Kwara-50

Abia-47

Kaduna-35

Benue-34

Oyo-26

Ebonyi-24

Kano-16

Niger-15

Anambra-14

Gombe-12

Edo-11

Rivers-6

Nasarawa-5

Delta-5

Borno-3

Enugu- 2

Bauchi-2

Kebbi- 1

Kamar yadda hukumar NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter, a yanzu jimillar mutane 37,225 ne ke dauke da cutar wadanda kuma suke kwance a gadon asibiti.

Haka zalika, hukumar ta sanar da cewa, akwai jimillar mutane 15,333 da aka sallama daga asibiti bayan samun tabbacin warkewa daga cutar.

A hannu daya kuma jimillar mutane 801 ne suka mutu sakamakon wannan cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel