Gwamnatin tarayya ta gabatar da N12.7tr a matsayin kasafin 2021 na kasar

Gwamnatin tarayya ta gabatar da N12.7tr a matsayin kasafin 2021 na kasar

Gwamnatin tarayya ta ce tana hasashen gabatar da N12,658,009,802,283.00 a matsayin kasafin kudin kasar na 2021. Gwamnatin ta ware N5.16trn a matsayin rarar kasafin na 2021 wanda ya haura N4.98trn da aka samu a kasafin 2020.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar taswirar kasafin mai taken MTEF/FSP wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar dattijai a ranar Talata.

Gwamnatin tarayyar ta kuma tsayar da kudin danyen mai na shekarar 2021, $40 akan kowacce gangar mai da kuma canjin N360 akan kowacce dala.

A cewar takardar, kudaden da aka yi hada hadarsu sun kai N481bn, ana bin kasar bashin N3.12trn, sai kudin da aka ware don biyan bashin N220bn da kuma N5.7 kudin fansar kaya da ayyuka.

Gwamnatin ta kuma ware N3.33trn a matsayin kudaden da aka ware don gudanar da ayyukan kasar.

Gwamnatin na hasashen samun N500bn daga bangaren kudaden harajin sitamfi, sabanin N200bn da aka samu a shekarar 2020.

Gwamnatin ta yi nuni da cewa an ware N4.31 a matsayin kudaden jami'ai da fansho, karin N724.67bn akan na shekarar 2020.

Kudaden jami'ai, na ci gaba da karuwa a kowacce shekara sakamakon yawaitar daukar ma'aikata da hukumomin gwamnati ke yi, wasu lokutan ba tare da bin ka'ida ba.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Gwamnatin Jigawa ta soke bukukuwan babbar Sallah

Gwamnatin tarayya ta gabatar da N12.7tr a matsayin kasafin 2021 na kasar
Gwamnatin tarayya ta gabatar da N12.7tr a matsayin kasafin 2021 na kasar
Asali: Facebook

Gwamnati tayi gargadin cewa bisa hasashen kashi 70 na harajin da za a tattara na 2021, ba lallai bane a iya biyan kudaden jami'an.

Gwamnatin ta kuma yi hasashen hako ganga 1.88m ta danyen mai a kowacce rana a 2021 sabanin 1.80mbpd na kasafin shekarar 2020.

A wani labarin kuwa, Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya soke bukukuwan babbar Sallar Lahya a jihar da kuma dakatar da sarakuna biyar masu daraja na jihar daga jagorantar duk wani hawan Sallah ko hawan daushe a babbar Sallar wannan shekarar.

Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

A tattaunawar, ya ce wannan umurnin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na ci gaba da yaki don dakile yaduwar cutar COVID-19.

Ya bayyana cewa, jihar a yanzu ta samu gagarumar nasara ta wannan fuskar, kasancewar bata samu bullar cutar ba kusan kwanaki 30 yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel