'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)

'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)

Bincikar 'yan siyasa a Najeriya wani babban al'amari ne. Su kan kirkiro dabaru a tunaninsu hakan zai sa su tsallake hukunci.

Idan a kotu ne, suna zuwa da abubuwa masu tarin yawa, daga ciki kuwa akwai abubuwan da suka danganci lafiya. Daga nan ne sukan nemi hanyar ficewa kasashen ketare don duba lafiyarsu.

A kalla 'yan siyasa 5 ko jami'an gwamnati ne suka bayyana da ciwo a yayin da ake bincikarsu a kan handame kudin kasa. Ga labarinsu da hotunansu.

1. Olisa Metuh

Olisa Metuh tsohon kakakin gagarumar jam'iyyar adawa ne ta PDP. Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ce ta gurfanar da shi a 2016.

EFCC na zarginsa da karbar N400 miliyan daga ofishin mai bada shawara a kan tsaron kasa. Metuh ya yi ikirarin bashi da lafiya kuma ya bukaci kotu da ta bashi damar tafiya kasar ketare asibiti, lamarin da kotun ta hana shi.

Daga bisani, ya daina zuwa kotu saboda rashin lafiya kamar yadda lauyoyinsa suka ce. A watan Fabrairun 2018, Metuh ya isa kotu a motar asibiti. Lauyansa ya ce an kwantar da shi a asibitin Nnamdi Azikiwe da ke Nnewi a jihar Anambra.

Ya fadi inda ya suma yayin da ya tunkari wurin ajiye wadanda ake tuhuma a kotu, lamarin da yasa lauyansa ya bukaci a janye shari'ar.

Mai shari'a Okon Abang ya jaddada cewa sai an ci gaba. A watan Fabrairun 2020, kotun ta yankewa Metuh shekaru 39 a gidan gyaran hali.

'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)
'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna). Hoto daga BBC Pidgin
Asali: UGC

2. Bello Haliru Mohammed

A 2016, tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Bello Haliru Mohammed ya bayyana a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan keken guragu ta asibiti a yayin da ake shari'arsu.

EFCC ce take zargin Haliru da dan sa da karbar $2 biliyan daga cikin kudin makamai a zamanin da Sambo Dasuki yake mai bada shawarar tsaron kasa.

'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)
'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna). Hoto daga BBC Pidgin
Asali: UGC

3. Dino Melaye

Tsohon sanatan Najeriya, Dino Melaye, ya shiga hannun 'yan sanda a watan Afrilun 2018 a kan zarginsa da ake da hada kai wurin aikata laifi tare da mallakar makamai bayan wasu wadanda ake zargi sun ce shi ke samar musu da makamai.

Amma kuma, ya fito daga motar 'yan sanda da ke tafiya yayin zuwa kotu a Lokoja. Lamarin da yasa suka kare a asibitin Zankili da ke Mabuchi a Abuja. Daga bisani an mayar da shi asibitin kasa da ke Abuja kafin garzayawa wata kotun Majistare.

Bayan an bada belinsa, 'yan sanda sun sake cafkesa inda aka mayar da shi jihar Kogi domin amsa sabbin tambayoyi. Kotun ta hana belinsa inda ta bukaci a adana shi a gidan yari na makonni biyar.

Amma kuma a kowanne zaman kotu, Melaye na bayyana a motar asibiti, kwance a kan gadon daukar marasa lafiya da ido rufe.

'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)
'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna). Hoto daga SUMNER_SAMBO
Asali: Twitter

4. Abdulrasheed Maina

Sannanen jami'in gwamnati ne kuma tsohon shugaban hukumar fansbo ta kasa. EFCC ce ta gurfanar da shi a kan zargin rub da ciki a kan N2 biliyan na 'yan fansho da wata N100 biliyan.

Tsohon shugaban hukumar fanshon ya koka a gaban wata babbar kotun tarayya a kan cewa bashi da lafiya. Daga nan ya ci gaba da bayyana a kan keken guragu don jaddada ikirarinsa.

A kan rashin lafiyarsa, ya bukaci a bada belinsa wanda aka bada. Amma kuma yana garkame saboda rashin cika sharuddan belinsa.

'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)
'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna). Hoto daga BBC Pdigin
Asali: UGC

5. Kemebradikumo Pondei

Na kwanan nan shine Farfesa Kemebradikumo Pondei, manajan daraktan kwamitin rikon kwarya na hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta.

A ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, Pondei ya suma a yayin da ake bincikar sa a gaban majalisar tarayya.

An kafa wani kwamitin ne a majalisar wakilai don bincikar NDDC a kan badakalar wasu makuden kudade da ake zargin hukumar da yi.

Yana tsaka da amsa tambayoyin da ake masa ne ya shide.

'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)
'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna). Hoto daga Azubike Osimili
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo da hotuna: An yi jana'iza tare da birne Isma'ila Funtua a Abuja

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel