Bidiyo da hotuna: An yi jana'iza tare da birne Isma'ila Funtua a Abuja

Bidiyo da hotuna: An yi jana'iza tare da birne Isma'ila Funtua a Abuja

An birne gogaggen dan siyasa kuma makusanci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Isma'ila Isa Funtua a Abuja.

Funtua, wanda siriki ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma babban abokinsa, ya rasu a Abuja a ranar Litinin.

An birnesa a makabartar Gudu, bayan sallatar gawarsa da aka yi a babban masallacin Shehu Shagari da ke Area 1, Garki, a garin Abuja.

Wasu daga cikin jiga-jigan da suka samu halartar jana'izar sun hada da Mamman Daura, dan uwa kuma makusancin shugaan kasa Muhammadu Buhari

Akwai Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe; Nduka Obaigbena, shugaban gidan jaridar THISDAY da ARISE TV; da Sam Nda-Isaiah, mwallafin jaridar Leadership.

Gwamnan jihar Yobe tare da Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, duk sun halarta.

Bidiyo da hotuna: An yi jana'iza tare da birne Isma'ila Funtua a Abuja
Bidiyo da hotuna: An yi jana'iza tare da birne Isma'ila Funtua a Abuja. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel