Yadda Isma'ila Funtua da wasu suka so sasanta wa da ni a yayin da nake tsare - Sowore
Wakilan shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka samu jagorancin Isma'ila Isa Funtua, sun yi kokarin yi wa Omoyele Sowore magana a lokacin da aka tsaresa na sama da watanni hudu a 2019, mawallafin jaridar Sahara Reporters ya sanar a ranar Talata.
Sowore ya tuna yadda al'amarin ya faru a yayin da Funtua, makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma minista a jamhuriya ta biyu, ya rasu a ranar Litinin.
A wata tattaunawa da Sowore yayi da gidan Talabijin na Sahara, ya ce wakilan da suka samu jagorancin Funtua sun je don tattaunawa a kan yadda za a sako shi bayan tsaresa da aka yi.
Amma Sowore, tsohon mai rajin kare hakkin dalibai, wanda ya yi gwagwarmaya a mulkin soja kuma ya yi fama da hare-hare, ya ce ya yi watsi da wannan tayin.
"Ba za ka iya nasara a kan gwamnati ba," yace tsohon dan siyasar wanda yake daya daga cikin na hannun saman shugaban kasar ya sanar da shi.
"Toh, babu dadewa za ka san cewa jama'a na iya nasara a kan gwamnati, komai karfin rinjayen gwamnatin da kake tunani," yace ya bada martani tare da tabbaci.
KU KARANTA: Boko Haram: Modu Sulum, sabon kwamanda mai matukar hatsari
Sowore, wanda ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 da ya gabata kuma ya sha mugun kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanar da hakan ne shafinsa na Facebook.
Ya ce wani wakilin mai suna Nduka Obaigbena, mawallafiin jaridar ThisDay, ya yi kokarin jan hankalinsa amma ya ki tankwasuwa.
A wannan lokacin, jaridar Premium Times ta ruwaito yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wakilansa don shawo kan mai rajin kare hakkin dan Adam din kafin a sako shi.
Wakilan shugaban kasar da suka ziyarci Sowore a wannan lokacin da yake tsare kamar yadda yace, sun je ne don kawo lumana. Ya yada makamansa don samun zaman lafiya ya tabbata sannan a sako sa.
Baya ga marigayi Funtua da Obaigbena, sauran da suka shiga cikin sasancin sun hada da mawallafin jaridar Vanguard, Sam Amuka da kuma mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, cewar Sowore.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng