Bidiyo: Sojoji sun lakaɗawa wani mutum duka a Abiya

Bidiyo: Sojoji sun lakaɗawa wani mutum duka a Abiya

Wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu sojoji biyu suka yi wa wani mutum duka tsiya har sai da ta kai ga ya fada wata magudanar ruwa.

A faifan bidiyo da ya ke ci gaba da shawagi a dandalan sada zumunta, an jiyo sautin muryar wadanda suka shaidi lamarin ta hanyar gani da ido, suna cewa sojojin su yi rangwami domin mutumin dattijo.

Dakarun sojin Najeriya
Hoto daga jaridar Premium Times
Dakarun sojin Najeriya Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

Sai dai har kawo yanzu, manema labarai ba su iya tabbatar da dalilin ya sanya sojojin suka lakaɗawa wannan mutum dukan tsiya ba.

Kafofin watsa labarai da dama sun wallafa rahoton wannan bidiyo, inda aka hangi daya daga cikin sojojin yana haurin mutumin da kafa.

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, an tabbatar da mutuwar mutane 7 a sabon rikicin da ya barke a kauyen Gan da ke zangon Kataf a jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa, reshen karamar hukumar Zangon Kataf, Fasto Isaac Ango Manama ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Leadership a ranar Talata.

KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun kama ɓarayin babur a jihar Ogun

Ya ce maharan da suka kai farmaki kauyen da misalin karfe 7:00 na yamma sannan suka fara harbe-harbe sun wuce mutum 50.

Ya ce a halin yanzu an samu gawawwakin mutum takwas kuma suna babban asibitin Zo kwa yayin da wasu kauyawan suka bace.

"Ina kira ga jama'a da su kira wakilansu da basu jajanta musu ba a kan wannan kaddarar.

"Har yanzu babu dan majalisar jihar da ya ziyarci sansanin, hakan nuni ne da cewa basu damu da damuwarmu ba," in ji shi.

Sakataren sansanin 'yan gudun hijira na Zonkwa, Ezekiel James ya bayyana cewa ya yi wa mutum 559 rijista da suka tsere daga kauyukan da ke da makwabtaka da su.

Ya kara da cewa sansanin na matukar bukatar magunguna da ababen amfani. Ya yi kira ga masu hali da su tallafa wa wadannan 'yan gudun hijira.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel