‘Yan sanda sun kama ɓarayin babur a jihar Ogun

‘Yan sanda sun kama ɓarayin babur a jihar Ogun

A ranar Litinin 20 ga watan Yuli, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun, ta samu nasarar dakume wasu mutum biyu da ake zargi da ta'adar fashin da makami.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, ababen zargin biyu sun yi kaurin suna a kan ta'addancin kwacewa al'umma babura da suka addabi yankin Ijebu-Ode da sauran kewaye.

An damke mutanen biyu a yayin da suka kokarin kwacen wani babur bayan sun kwace wa wasu 'yan Achaba biyu baburansu na neman na abinci.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin.

‘Yan sanda sun kama ɓarayin babur a jihar Ogun
Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Punch
‘Yan sanda sun kama ɓarayin babur a jihar Ogun Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Punch
Asali: Twitter

Oyeyemi ya ce an kama matasan biyu, Joshua Michael mai shekaru 27 da kuma Emeka Nwanga mai shekaru 26 bayan da wani ma'aikaci Sufeta Olusesi Kayode ya shigar da korafi a ofishin 'yan sanda na Ilesa Ijebu.

Ya ce an ankarar da jami'an 'yan sandan cewa wasu 'yan fashi da makami na kokarin yin ƙwacen wani babur a Unguwar Ikangba.

A yayin da ma'aikata suka kai kora yankin, matasan biyu sun ranta a na kare yayin da suka hangesu. An yi sa'a mutanen gari suka yi musu tara-tara a ka cikwikwiyesu inji kakakin rundunar 'yan sandan.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Babban Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya ce an yi wa jami'an 'yan sanda ƙarin girma wanda yawansu ya kai 41,863 a cikin watanni 19 da suka gabata.

KARANTA KUMA: Sauran ƙiris a buɗe makarantun Islamiya a Kano - Gwani Yahuza

Mista Adamu ya fayyace hakan ne a ranar Litinin yayin bikin ɗaga likafar wasu mayan jami'an 'yan sanda 10 da aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito Adamu ya ce: "Tun daga lokacin da na karbi akalar jagoranci ta hukumar 'yan sandan Najeriya a watan Janairun 2019, an yi wa jami'an 'yan sanda 41,863 zuwa matsayi na gaba.

Ya ce tsarin ɗaga likafar jami'an wata dabara ce ta kara wa jami'an karfin gwiwa da kuma karsashin ma'aikata wajen matsalolin tsaro na cikin gida.

Mista Adamu ya ce ana gudanar da shirin ɗaga likafar ma'aikatan ne bisa la'akari da tsari da kuma cancanta gami da kwarewa da kwazo a kan aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel