Abubuwa 11 da baku sani ba game da shugaban NDDC, Farfesa Daniel Pondei

Abubuwa 11 da baku sani ba game da shugaban NDDC, Farfesa Daniel Pondei

Daniel Kemebradikumo Pondei, Farfesa a fannin magunguna daga jami'ar Niger Delta (NDU) da ke Bayelsa, ya samu mukamin shugabancin hukumar bunkasa Niger Delta a ranar 19 ga watan Fabreru, 2020. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada shi wannan mukami.

Ga wasu abubuwa 11 da ya kamata ku rinka tunawa da shugaban hukumar ta NDDC, wanda ya yanke jiki ya fadi a gaban kwamitin bincike na majalisar tarayya a ranar Litinin.

1. A shugabancin hukumar NDDC, Pondei ne ya maye gurbin Joi Nunieh, 'yar asalin garin Ogoni kuma lauya, wacce diyace ga lauyan farko na garin Ogoni.

2. Ya karbi ragamar shugabancin NDDC a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabreru, a shelkwatar hukumar da ke Fatakwal.

3. Farfesa Pondei ya kammala karatun digiri na farko a fannin likitanci, bangaren tiyata MMBS a jami'ar Lagos, daga nan ya wuce jami'ar Nottingham inda ya karanci Microbiology.

4. Ya yi karatu a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Fatakwal, kuma ya kasance malamin jami'a tun daga 2001. Ya kasance kwararre a masana'antar bincike da malunta.

5. Pondei ya bayyana kansa a matsayin "kwararre a fannin 'epidemiology', kimiyyar rayuwa, binciken bayanai, kwarewar shirye shirye da kuma koyarwa," a shafinsa na Linkedin.

6. Ya gabatar da makala karo ta 36 a jami'ar NDU a ranar 17 ga watan Afrelu 2019, mai taken, "Kwayoyin cuta: An wofantar dasu, illolin da suke dashi idan aka yi watsi da su."

7. Pondei ya rike mukamin shugaban sashen likitancin kananan halittu da kuma shugaban sashen karatun ilimin kimiyyar likitanci, a kwalejin kimiyyar kiwon lafiya ta NDU.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Mutane 562 sun sake kamuwa da cutar COVID-19 a Nigeria

Abubuwa 11 da baku sani ba game da shugaban NDDC, Farfesa Daniel Pondei
Abubuwa 11 da baku sani ba game da shugaban NDDC, Farfesa Daniel Pondei
Asali: Twitter

8. Tsohon shugaban kungiyar likitoci NMA reshen jihar Bayelsa ya rike mukamin shugaban kwamitin kungiyar NMA na kasa a bangaren bincike.

9. Ya kasance mamba a kwamitin shirin inshorar lafiya ta jihar Bayelsa da ke wakiltar ra'ayin al'umma. Ya yi rubuce rubuce da dama kuma yafi sha'awar fannin cutuka masu hatsari.

10. Farfesa Kemebradikumo Pondei, da tawagarsa a ranar 16 ga watan Yuli, sun fice daga zauren kwamitin bincike na majalisar tarayya inda ake tuhumar badakalar N40bn da aka tafka a NDDC.

11. A ranar 20 ga watan Yuli, Pondei ya yanke jiki ya fadi gaban kwamitin bincike na majalisar tarayyar, a lokacin da yake amsa tambayoyi kan badakalar

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng