An kubutar da Almajirai 15 daga wata cibiyar azabtarwa a jihar Neja

An kubutar da Almajirai 15 daga wata cibiyar azabtarwa a jihar Neja

An gano wata cibiya da aka killace Almajirai ana azabtar da su cikin wani yanayi na cin zarafin bil Adama a jihar Neja kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An kubutar da Almajirai 15 daga cibiyar wadda aka rika a matsayin makaranta ta horar da kananan yara.

Cibiyar wadda take Unguwar Gwari a garin Suleja, tana kunshe da Almajirai daga kan 'yan shekaru biyar, inda galibinsu suka nuna alamun an dade ana azabtar da su.

Akwai raunuka iri-iri a gadon bayansu yayin da wasunsu aka kubutar da su yayin da suke daure da sarka a kafafunsu.

Babban Sufeton 'Yan sanda
Babban Sufeton 'Yan sanda
Asali: Facebook

Jami'an 'yan sanda sun tsinto karafa daban-daban da ake amfani da su wajen yi wa yaran azaba iri-iri yayin da suka kai simame cibiyar bayan da makwabta suka shigar musu da korafi.

'Yan sanda sun cafke mamallakin cibiyar Umar Ahmed, mai shekaru 46 yayin da suka kai simame.

Jami'in hulda da al'umma na hukumar 'yan sandan jihar, ASP Abiodun Wasiu, ya tabbatar da wannan lamari da cewa 'yan sandan ofishin Suleja sun ceto yara 15 daga cibiyar.

Ya ce tuni an mika yaran Hukumar Kare Hakkin Yara ta jihar, inda kuma bincike zai ci gaba da kankama.

Ya kara da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Litinin ne wuta ta babbake sabon ginin da aka kammala a ofishin hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS) reshen jihar Katsina.

Gobara ta tashi a ofishin FIRS da ke kallon filin wasa na Muhammadu Dikko da misalain karfe 12:08 na ranar Litinin, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta rawaito.

KARANTA KUMA: Ina yi wa Ministan harkokin waje fatan samun waraka cikin gaggawa - Buhari

Har ya zuwa lokacin da 'The Nation' ta wallafa rahotonta, jami'an hukumar kashe gobara suna kokarin kashe wutar da ke ci a ofishin.

Kimanin makonni biyu kenan da gobara ta tashi a babban bankin Najeriya dake jihar Gombe a ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2020.

Sahara Reporters ta samu rahoto daga wata majiya cewa gobarar ta fara ci ne da misalin karfe 10 na safe.

Wannan ya shiga cikin jerin gobara da aka samu a ma'aikatun gwamnati a fadin tarayya cikin yan watannin nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel