COVID-19: An soke taron bayar da kambun kwallo na Ballon d’Or 2020
- Masu shirya taron bada kambun karramawa na kwallon kafa mai taken 'Ballon d'Or' a ranar Litinin, sun soke taron na wannan shekarar
- An soke bayar da kambun 'Ballon d'Or' ne sakamakon annobar Coronavirus da ta tilasta dakatar da kakar wasanni da dama ciki har da 'French League 1'
- Wannan shine karo na farko da aka soke taron bada kambun ga zakarun 'yan kwallo, tun bayan fara taron a shekarar 1956
Sakamakon yanayin da duniya take ciki na annobar Coronavirus, masu shirya taron bada kambun karramawa na kwallon kafa mai taken 'Ballon d'Or' a kasar Faransa, a ranar Litinin, sun soke taron.
Wannan shine karo na farko da aka soke taron bada kambun ga zakarun 'yan kwallo, tun bayan da Stanley Matthews ya lashe kambun a shekarar farko na taron a 1956.
"Ba za a bayar da kambun a wannan shekarar ta 2020 ba, saboda yanayin da ake ciki, hakan ba zai yiyu ba," cewar Pascal Ferre, alkalin mujallar.
Cutar Covid-19 ta tilasta dakatar da gasar wasannin kwallon kafa da dama tun a matan Maris, inda gasar Bundesliga ta fara dawowa a watan Mayu.
Kungiyar shirya kwallon kasar Faransa ta ce zai zama rashin adalci a zabi dan wasan da yafi kowa a duniya alhalin an soke gasar kwallaye ciki har da 'French Ligue 1'.
KARANTA WANNAN: FG ta kaddamar da rabon N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara
"Muna da yakinin cewa irin wannan shekarar... ya kamata mu dauketa a matsayin ta daban," a cewarsa.

Asali: Twitter
"Watanni biyu (Janairu da Fabreru), cikin watanni goma sha daya da ake bukata domin tantance wadanda zasu dauki kambun, sun isa su dakatar da taron karramawar."
Lionel Messi ne ya lashe kambun gasar ta Ballon d'Or a shekarar da ta gabata, a karo na shida ba tare da kuskurewa ba.
A bangaren mata kuwa, da aka fara bada kambun a shekarar 2018, an soke taron na wannan shekarar.
Kungiyar ta kuma kara da cewa tana dakon shekarar 2021 domin gudanar da taron bayar da kambun, amma dai zata gudanar da taro ne na jefa kuri'a kan zakarun 'yan kwallon da suka dade ana damawa da su.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng