Yanzu-yanzu: Ministan Buhari ya bayyana gaban kwamitin bincike

Yanzu-yanzu: Ministan Buhari ya bayyana gaban kwamitin bincike

Godswiil Akpabio, ministan kula da harkokin Neja Delta, ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai don bincike a kan al'amarin hukumar kula da cigaban yankin (NDDC).

Ministan ya halarci zauren majalisar ne a daidai karfe 11:20 na safiyar ranar Litinin.

Kwamitin majalisar ya kira Akpabio ne bayan da Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar, ta bayyana wasu zarge-zarge a kan shi a ranar Juma'a.

Nunieh ta ce a yayin da take shugabantar hukumar, ya bukaceta da ta kashe N10 biliyan a matsayin tallafin Kirsimeti.

Ta ce, kin cika wannan umarnin ne yasa aka sallameta daga kujerarta.

Ta zargi Akpabio da kwace dukkan bayanan kashe kudi na hukumar kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni.

"Abu na farko da na fara yi shine rubuta wasika kuma da kanshi ya bani abinda zan rubuta a ciki. A wannan wasikar, ya bukaceni da in rubuta dukkan kamfanonin da Sanata Nwaoboshi ke da su," yace.

Ana zargin hukumar ne da watanda da kudi har N40 biliyan.

Yanzu-yanzu: Ministan Buhari ya bayyana gaban kwamitin bincike
Yanzu-yanzu: Ministan Buhari ya bayyana gaban kwamitin bincike. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Duniya labari: Duba hotunan tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida

A wani labari na daban, majalisar wakilan Najeriya ta bada umarnin damko mukaddashin manajan daraktan kwamitin rikon kwarya na hukumar habaka yankin Neja Delta, Farfesa Kemebradikumo Pondei a kan yadda ya fice daga majalisar babu izini.

Idan za mu tuna, ana bincikar pondei ne a kan wasu miliyan N40 da suka yi batan dabo a hukumar, ya fice daga majalisar a ranar Alhamis yayin da ake bukatar jin ta bakinsa.

Shugaban NDDC ya zargi shugaban kwamitin majalisar wakilan masu alhakin bincikarsu, Olubunmi Tunji-Ojo, da rashawa.

A yayin jawabi ga kwamitin, Pondei ya ce, "Mu a NDDC ba mu amince da shugaban kwamitin binciken nan ba.

"Ana zarginsa da saka siyasa a al'amuransa. Yana saka siyasa kuma mun tabbatar da cewa ba za a mana adalci ba."

"Ba mu da matsala a kan bayanin da aka bukace mu mu yi da kuma bayyana gaban kwamitin wucin gadin. Amma matukar yana nan, babu wani bayani da za mu yi," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel