Zaben Ondo: Mutum 4 sun janye wa Akeredolu takara yayin da aka fara zaben fidda gwani

Zaben Ondo: Mutum 4 sun janye wa Akeredolu takara yayin da aka fara zaben fidda gwani

- Gwamna Rotimi Akeredolu ya sake samun karfin gwiwa a kan kudirinsa na neman tazarce

- Mutum hudu da ke neman tikitin takara a jam'iyyar APC sun janye wa gwamna Akeredolu

- Za a gudanar da zaben fidda gwanin takarar a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli

Neman wa'adi na biyu da gwamna Rotimi Akeredolu ya sa gaba, ya sake samun karfin gwiwa yayin da mutum hudu suka janye masa takara ana gaf da fara zaben fidda gwani.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, mutum hudu da ke hankoron tikitin takara na jam'iyyar APC, sun janye jiki domin goyon bayan gwamna Akeredolu.

A yayin da bai wuci 'yan sa'o'i kalilan ba a fara zaben fidda gwani a ranar Litinin 20 ga watan Yuli, Ife Oyedele ya janye takararsa domin marawa gwamnan mai ci baya.

Rotimi Akeredolu
Hoto daga Vanguard
Rotimi Akeredolu Hoto daga Vanguard
Asali: Depositphotos

Da yake ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli, Oyedele wanda shi ne babban daraktan kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Delta, ya ce a yanzu ya koma tafiyar gwamna Akeredolu.

Haka zalika wasu mutum uku sun janye wa Akeredolu takara da suka hadar da; Olusegun Abraham, Jimi Odimayo da kuma Dr Nathaniel Adojutelegan.

Jerin wadanda a yanzu suke neman tikitin takarar na jam'iyyar APC sun hadar da; Olusola Oke (SAN), Segun Abraham, Olaide Adelami, Bukola Adetula, Jumoke Anifowose, Sola Iji, Isaac Kekemeke da Awodeyi Akinsehinwa.

KARANTA KUMA: Jam'iyyu 35 za su goyi bayan Obaseki a kan naira miliyan biyar-biyar - APC

Sai dai tababa ta baibaye tsarin zaben fidda gwanin yayin da dukkanin manema takarar suka zabi tsarin gudanar da zaben ta hanyar 'yar tinke a madadin amfani da wakilai in banda gwamna Akeredolu.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ba magoya bayan jam’iyyar tabbacin nasara a zaben gwamnan Edo mai zuwa.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a Edo a karshen mako, ya nuna karfin gwiwar cewa jam'iyyar APC za ta yi nasara a zaben wanda za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Da yake hannunka mai sanda ga Godwin Obaseki, gwamnan jihar mai ci na jam'iyyar PDP, Oshiomhole ya ce ya yi farin ciki da cewar “Allah ya fitar da maciji.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel