Jam'iyyu 35 za su goyi bayan Obaseki a kan naira miliyan biyar-biyar - APC

Jam'iyyu 35 za su goyi bayan Obaseki a kan naira miliyan biyar-biyar - APC

Jam'iyyar APC reshen jihar Edo, ta zargi gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP, da samun goyon bayan wasu jam'iyyu 35 ta hanyar saye 'yancinsu a zaben gwamnan jihar mai zuwa.

Kwamitin sadarwa na yakin neman zaben jihar Edo na jam'iyyar APC, ya yi zargin cewa, wasu jam'iyyu 35 sun goyi bayan kudirin takarar Gwamna Obaseki a kan biyan kowannensu naira miliyan biyar-biyar.

Haka kuma kwamitin ya bayyana cewa, akwai alkawarin naira miliyan 65 da za a bai wa jam'iyyun 35 domin tabbatar da nasarar Obaseki a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Jagoran Kwamitin, Prince John Mayaki, ya yi zargin cewa, jam'iyyu 'yan kuci-ku-bamu, sun gudanar da wani taro a karshen makon da ya gabata domin tumke damarar sayar da martabarsu ta hanyar goyon bayan gwamna Obaseki.

John Mayaki ya yi babatu da cewa goyon bayan Obaseki da jam'iyyun suka yi ta wannan siga, wulakantar da kai ne gami da sayar da 'yancinsu na kasancewa jam'iyyu masu mutunci.

Godwin Obaseki
Godwin Obaseki
Asali: Twitter

A yayin da jam'iyyun ke ikirarin goyon bayan gwamna Obaseki domin ya tisa kyakkyawan kwazon da yayi a kan kujerar mulki, shi kuma Mayaki ya misalta lamarin a matsayin abin kunya mai munin gaske.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, baya ga jam'iyyar PDP da APC da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta bai wa lasisin damawa a zaben gwamnan jihar, akwai wasu jam'iyyu 12 da suka samu wannan 'yanci.

Jam'iyyun sun hadar da; Action Alliance (AA), African Democratic Congress (ADC), African Democratic Party (ADP), All Progressives Grand Alliance (APGA), Allied Peoples Movement (APM) da All Peoples Party (APP).

Sauran jam'iyyun sune; Labour Party (LP), New Nigeria Peoples Party (NNPP), National Rescue Movement (NRM), Social Democratic Party (SDP), Young Progressive Party (YPP) da Zenith Labour Party (ZLP).

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta zargi ‘dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, Osagie Ize-Iyamu da yin karya game da zargin yadda Gwamna Obaseki ya samu tikiti a PDP.

KARANTA KUMA: Buhari ya tsawaita wa'adin shugaban Hukumar NSCDC

Fasto Osagie Ize-Iyamu ya fito ya na cewa jam’iyyar PDP ta saida tikitin takarar gwamnan jihar Edo ga Godwin Obaseki ne bayan ya biya kudi Naira biliyan 15.

Majalisar yakin neman zaben PDP na jihar Edo ta karyata wannan zargi, ta ce sam babu burbushin gaskiya a kan abin da ‘dan takarar hamayyar ya fada.

Shugaban kwamitin yada labarai na jirgin yakin PDP a zaben na Edo, Cif Raymond Dokpesi ya yi magana a garin Fatakwal, jihar Ribas, inda ya musanya wannan batu.

Raymond Dokpesi tare da wasu manyan PDP irinsu Sanata Dino Melaye sun yi jawabi da cewa babu inda gwamna Obaseki zai samu wannan makudan kudi da zai bada.

Dokpesi ya ke cewa abin mamaki ne Ize-Iyamu wanda ya yi takarar gwamna a karkashin PDP a 2016 ba tare da ya bada ko sisin kobo ba, ya fito ya na irin wannan furuci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel