'Yar sanda da ɗiyarta sun faɗa tarkon masu garkuwa da mutane a Kaduna

'Yar sanda da ɗiyarta sun faɗa tarkon masu garkuwa da mutane a Kaduna

Ana zargin masu ta'adar garkuwa da mutane, sun yi awon gaba da wata jami'a ta 'yan sanda, ɗiyarta da kuma wasu mutum hudu a unguwar Janruwa da ke hanyar Patrick Yakowa a jihar Kaduna.

Wannan mummunan lamari kamar yadda wani bayar da shaida ya tabbatar ya bayyana cewa, ya auku ne da misalin karfe 10.00 na daren ranar Asabar da ta gabata.

Mutumin da yake bada shaidar; Babalola Mathew, ya ce 'yan ta'adda sun shigo unguwar cikin duhun dare inda suka afka wasu gidaje hudu salin alin cikin sanda.

Mista Mathew yace 'yan ta'addan sun yi awon gaba da mutum shida da suka hadar da babbar mace daya, wasu 'yan mata biyu, matasa biyu da kuma wani dattijo daya.

Yayin da manema labarai suka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Muhammadu Jalige, ya sha alwashin tattaro duk wasu bayanai game da lamarin daga babban jami'in dan sanda na Unguwar Janruwa.

Babban sufeton 'yan sanda na Najeriya; Muhammadu Adamu
Babban sufeton 'yan sanda na Najeriya; Muhammadu Adamu
Asali: Facebook

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Hukumar sojin Najeriya ta ce dakarun rundunar Operation Lafiya Dole, sun yi nasarar durkusar da Boko Haram tare da ISWAP a yankin arewa maso gabas.

A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi daga babban jami'in hulda da al'uma na rundunar, Manjo Janar John Enenche ya ce bayan bayanan sirrin da suka samu, sojin a ranar 17 ga watan Yuli sun yi niyyar samun 'yan ta'addan a ranar kasuwarsu.

Daga nan ne suka gano kai da kawowarsu a yankin Kolofata, wani gari mai iyaka da Kamaru inda dakarun ke zama.

KARANTA KUMA: Damuwa ta kashe mutum 3 yayin da gwamnatin Kaduna ta rushe gidaje 100 a Zariya

Sun kashe 'yan ta'adda shida da ke kokarin tsallakawa zuwa Kamaru ta sashen Sambisa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma ce dakarun sun tsinto bindigu 3 kirar AK 47, harsasai, mota kirar Honda Salon, babur daya, kekuna takwas, wayoyi uku da layikan waya da Qur'anai biyar.

Ya kara da cewa rundunar ta halaka manyan shugabannin 'yan ta'addan takwas a yayin da suka yi yunkurin shiga sansanin sojin da ke Damasak.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel