Damuwa ta kashe mutum 3 yayin da gwamnatin Kaduna ta rushe gidaje 100 a Zariya

Damuwa ta kashe mutum 3 yayin da gwamnatin Kaduna ta rushe gidaje 100 a Zariya

Akalla mutum uku ne ake fargabar rai ya yi musu halinsa, yayin da Hukumar Tsare-Tsare da Ci gaba ta jihar Kaduna (KASUPDA), ta rushe fiye da gida 100 a Unguwar Bare Bari da ke karamar Hukumar Zariya ta jihar.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, wani rahoto da Arewa Agenda ta wallafa ya bayyana yadda mutum uku suka yi gamo da ajali saboda shiga cikin tsananin damuwa da kuma tsabagen baƙin ciki.

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa yayin zantawa da manema labarai sun bayyana cewa, matakin da KASUPDA ta dauka bai biyo tafarkin dace ba kamar yadda shari'a tayi tanadi dangane da irin wannan lamari.

Yadda gwamnatin Kaduna ta rushe gidaje 100 a Zariya
Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Nigerian
Yadda gwamnatin Kaduna ta rushe gidaje 100 a Zariya Hakkin mallakar hoto; Jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

Mohammed Isa, daya daga cikin mutanen da aka rushewa gida ya ce: “A ranar 6 ga Yulin 2020 ne, Ma'aikatan KASUPDA sun fito ba zato ba tsammani kuma suka fara sanya alamar gidajen da zasu ruguje."

"A ranar Talata 7 ga wata, mun samu rahoto daga wata majiya cewa KASUPDA na shirin dauko jami'an tsaro domin su zameta garkuwa yayin ruguje gidaje."

"A yayin da suka bayyana da misalin karfe 9.00 na safe domin fara aiwatar da aikin na rusa, mutane suka tsaya kyam domin ganin hakan bai fary ba."

KARANTA KUMA: Coronavirus: Kar a buɗe makarantu har sai 2021 - ASUU

"Shugaban KASUPDA ya bai wa jami'an tsaro umarnin su harbi duk wanda ya tsaya musu a kan hanya amma aka yi sa'a jagoran jami'an tsaron mutum ne mai fahimta."

"Babban jami'in tsaron ya ce duk da an ba shi umarnin ya aiwatar da hakan, sai dai tausayi ba zai iya barin shi ya aikata hakan ba."

"Sai kawai ya janye jami'ansa suka gabansu."

"Ba tare da an yi aune ba, sun sake bayyana a da misalin karfe 12.05 na dare a ranar Laraba, inda suka kwantar da duk wasu gidaje da ke yankin kafin ketowar Al-Fijir."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel