Dakarun soji sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su, sun damke wadanda ake zargi

Dakarun soji sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su, sun damke wadanda ake zargi

Hedkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar sojin Operation WHIRL STROKE ta ceto mutu 34 da aka yi garkuwa da su, ta damke wasu da ake zargi da laifin garkuwa da mutane tare da samo miyagun makamai a jihar Binuwai.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a a garin Abuja.

Enenche ya ce, nasarorin da aka samu sun biyo bayan bayanan sirrin da suke samu ne a kan inda miyagun masu garkuwa da mutanen suke.

Sun dade suna addabar kauyen Igbom da ke gundumar Nenzev ta karamar hukumar Logo ta jihar Binuwai.

Kamar yadda yace, dakarun rundunar sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan wanda hakan ya kai ga kashe wani mutum daya mai suna Zwa Ikyegh, wanda bincike ya nuna shine shugaban kungiyar.

Daga nan wasu daga cikinsu sun tsere da raunika sakamakon harbin bindiga.

"Nasarar wannan arangamar ta sa an ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su wadanda suka shafe sama da wata daya a hannun miyagu.

"Dukkan wadanda aka ceto an mika su ga 'yan uwansu da ke karamar hukuamr Logo," yace.

Dakarun soji sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su, sun damke wadanda ake zargi
Dakarun soji sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su, sun damke wadanda ake zargi. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: A kan Maryam Yahaya, wani matashi ya sha fiya-fiya

Enenche ya ce dakarun sun samu kiran gaggawa a kan wani satar mutane da aka yi a Austoma da ke gundumar Mbanema na karamar hukumar Ukum.

Ya ce babu kakkautawa zakakuran sojin suka garzaya inda lamarin ya faru tare da kama mutum biyu da ake zargi.

A wani labari na daban, a wani hari na simame da 'yan daban daji suka kai jihar Katsina a ranar Asabar, ya salwantar da rayukan dakarun soji 16, yayin da 28 suka jikkata.

Da misalin karfe 6.13 na Yammacin ranar Asabar yayin da dakaru suka fita sintiri a yankin Shimfida na karamar hukumar Jibiya ta jihar, 'yan bindiga sun yi musu kwanton bauna, inda suka rika yi musu ruwan wuta daga wani saman tsauni.

Daga cikin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da Manjo, Kyaftin, da Laftanar kamar yadda wata majiya daga dakarun sojin ta shaidawa manema labarai na jaridar The Punch.

An tattaro cewa wasu 'yan ta'adda biyu sun raunata yayin da dakarun sojin suka yi yunkurin mayar da martani.

Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin rundunar sojin kasa, Kanal Sagir Musa, ya ce ba zai iya bayar da tabbaci ba kuma ba ya da ta cewa domin lokacin shi ne karo na farko da ya samu labarin harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel