Da duminsa: WAEC da Najeriya an cimma matsaya, an dage ranar fara jarabawa

Da duminsa: WAEC da Najeriya an cimma matsaya, an dage ranar fara jarabawa

Gwamnatin tarayya da hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta yamma, sun cimma matsayar sauya ranar jarabawa. A maimakon fara jarabawar a ranar 4 ga watan Augusta da ta sanar da farko, za a fara a ranar 5 ga watan Satumban 2020.

Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, wanda ya sanar da hakan a Abuja, ya ce wannan ne sakamakon taron gwamnatin tarayya da shugabannin hukumar a Najeriya wanda aka yi a ranar Litinin.

Sannan dukkan bangarorin sun amince da tuntubar kasashe hudu a kan sabuwar ranar fara jarabawar.

Ministan ya kara da cewa, gwamnatin ta bai wa masu makarantu nan da ranar 29 ga watan Yulin 2020 don cika sharuddan bude makarantu.

Ya ce mai'aikatar tare da hadin guiwar ma'aikatar ilimi, hukumar yaki da cutuka masu yaduwa za su fitar da sharuddan bude makarantu.

Daraktan yada labarai na ma'aikatar ilimi, Ben Bem Goong, a wata takarda, ya ce ana bukatar masu makarantun kudi da su shirya tare da bin dukkan ka'idojin.

Da duminsa: WAEC da Najeriya an cimma matsaya, an dage ranar fara jarabawa
Da duminsa: WAEC da Najeriya an cimma matsaya, an dage ranar fara jarabawa. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda maza 10 suka yi gwajin 'gwaninta' a kaina - Matashiya mai shekaru 19

Nwajuiba ya yi kira ga makarantu da su duba kansu da kansu sannan su tura abinda suka gani ga ma'aikatar ilimi kafin ranar 29 ga watan Yulin 2020.

"Daga nan za a tuntubi masu ruwa da tsaki don duba halin da ake ciki tare da saka ranar sake bude makarantu ko kuma akasin hakan," yace.

Ministan ya ce hukuncin bashi da dadi amma shine ya dace wajen tabbatar da cewa an bude makarantu ta yadda malamai da dalibai za a tabbatar da kariyarsu.

Kamar yadda yace, tun daga ranar Talatar makon da ya gabata, "mun ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a bangaren wandanda suka hada da dukkan kwamishinonin ilimi na dukkan jihohi, kungiyar mamallaka makarantu, shugabannin makarantun gaba da sakandire, wasu gwamnoni da abokan ci gaba."

"A bangaren WAEC, mun yi taro kuma mun amince da tuntubar sauran kasashe hudu a kan saka sabuwar ranar jarabawa.

"Muna godiya a kan hadin kan da dukkan masu ruwa da tsaki suka bamu ta hanyar bada shawarwarinsu a bangarori daban-daban," ministan yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel