Yanzu-yanzu: Kotu ta hana jami'an tsaro kama tsohuwar MD ta NDDC

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana jami'an tsaro kama tsohuwar MD ta NDDC

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Fatakwal, jihar Ribas, ta haramta wa 'yan sandan Najeriya ko wata hukumar tsaro kama tsohuwar mukaddashin manajan daraktan NDDC, Joy Nunieh.

A ranar Alhamis, 'yan sanda sun zagaye gidan Nunueh da ke Fatakwal, amma Gwamna Nyesom Wike ya datse hanzarinsu inda ya shiga har gidan ya fitar da ita zuwa gidan gwamnati.

A ranar Juma'a, Nunieh ta shigar da kara gaban kotu inda ta roka da a hana 'yan sanda sake yunkurin kama ta.

Mai shari'a E. Thompson, ya amince da bukatar da ta mika gaban kotun ta hannun lauyanta, Sylvester Adaka.

Kotun ta hana NDDC ko wata hukumar, kama Nunieh har sai an kammala sauraron abinda ake zarginta da shi.

Bayan da aka tuntubeta, Nunieh ta tabbatar da cewa ta samu kariya daga babbar kotun jihar Rivers.

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana jami'an tsaro kama tsohuwar MD ta NDDC
Yanzu-yanzu: Kotu ta hana jami'an tsaro kama tsohuwar MD ta NDDC. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsohuwa mai shekaru 75 ta yi 'wuf' da mijin diyarta bayan rabuwarsu (Hotuna)

Legit.ng ta ruwaito cewa, jami'an 'yan sandan Najeriya sun tsinkayi gidan Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar habaka yankin Neja Delta (NDDC), inda suka yi masa zobe.

Jami'an tsaron sun isa gidan ne da ke lamba 3, titin Owuru Creek, kusa da titin Herbert Macauley da ke tsohuwar GRA a Fatakwal, jihar Ribas a sa'o;in farko na ranar Alhamis.

Wannan ci gaba ya faru ne kafin isar Nunieh gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa da ke Abuja inda za ta amsa tambayoyi a kan ayyukan NDDC.

A yayin da jaridar The Cable ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Omoni Nnamdi don tsokaci, ya bukaci a kira sa nan da mintuna 30.

Akpabio da Nunieh sun bayyana a gaban kwamitin rikon kwarya na majalisar dattawa, inda ake bincikarsa a kan badakalar wasu kudade har N40 biliyan wanda kwamitin rikon kwarya na hukumar suka lamushe.

Amma kuma Nunieh ta ce ministan ya tabbatar da tsigeta ne saboda ta ki yin abinda yake so. Tsohuwar manajan daraktar NDDC ta bayyana zargi kala-kala game da ministan.

Ta zargesa da yunkurin lalata da ita. Nunieh ta zargi ministan da umartar ta da ta canza kudin asusun NDDC daga dala zuwa Naira. Ya bata umarnin sallamar shugaban lauyoyin hukumar saboda dan arewa ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel