Kabilar Idoma: Abubuwa masu bada mamaki game da wannan kabilar

Kabilar Idoma: Abubuwa masu bada mamaki game da wannan kabilar

Kabilar Idoma ce mafi girman Kabila ta biyu a jihar Binuwai kuma ta mamaye kananan hukumomi 9 na yankin yammacin jihar. Ana samun 'yan kabilar Idoma a Ado, Agatu, Apa, Obi, Ohimini, Ogbadibo, Oju, Okpokwu da Otukpo.

Duk da a wadannan kananan hukumomin ne ake samun 'yan kabilar, ana samun wasu daga cikinsu a sassan jihar Nasarawa da Cross Rivers.

Kamar sauran kabilun Najeriya, tarihin kabilar ba a rubuce yake ba. Kamar yadda sauran suke, tarihinsu ya dogara ne a kan al'ada da raye-raye.

Saboda 'yan kabilar na tashi a gidan yawa, su kan tashi da sanin al'adunsu tare da duk wani abu da ya jibanci kabilarsu.

Duk da akwai sarkakiya game da tarihin wannan kabilar, masana tarihi na cewa jama'ar kabilar sun zo ne daga yankin Apa da ke masarautar Kwararafa bayan rarrabewa da suka yi.

An gano cewa sun samu wurin zama a wurin 'yan kabilar Tiv kafin da yawa daga cikinsu sukan koma mazauninsu na yanzu har zuwa jihohin Nasarawa da Cross Rivers.

Auren Idoma

Duk da wasu daga cikin al'adun kabilar na kamanceceniya da na Ibo da wasu kabilun kudu maso gabas, akwai wasu abubuwa da suka banbanta su.

A wasu kabilun Idoma, bayan an biya sadakin budurwa, angon da 'yan uwansa suna kai kyautar zakara da kudi ga amaryar a ranar bikin.

A al'adance, idan budurwar ta karba, hakan na nufin ta amince. Idan kuwa ta ki karba, yana nufin bata amince ba.

Kabilar Idoma: Abubuwa masu bada mamaki game da wannan kabilar
Kabilar Idoma: Abubuwa masu bada mamaki game da wannan kabilar. Hoto daga Pulse ng
Asali: Twitter

Camfe-camfen Idoma

Zuwan addinan Kiristanci da Musulunci tare da sauran addinai yasa wasu kabilu suka fara zubar da camfe-camfensu amma banda kabilar Idoma.

Wani camfin da har yanzu yake nan shine Alekwu, wanda ake kira da aljanun magabatansa masu alakanta mamatansu da masu rayuwa.

Kamar yadda al'adarsu take, a duk shekara ana bikin 'Aje Alekwu'. A nan ne suke yin yanka don ta kai wa magabatansu.

'Yan kabilar Idoma sun amince da cewa Alekwu ke basu kariya daga zina, sata da kisan kai.

Abincin Idoma

Sanannen abu ne idan aka ce 'yan kabilar Idoma na da matukar son abinci. Suna yin biki duk shekara na abinci.

Daga cikin abincin da suka fi so akwai miyar Okoho. Ana miyar da fitaccen ganyen Okoho, naman daji da sauran abubuwan miya.

Launin Idoma

Launin da wannan kabilar suka fi so tuntuni shine Ja da baki a gargajiyance.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel