Yanzu: Majalisar tarayya ta gayyaci Ministan Niger Delta kan badakalar NDDC

Yanzu: Majalisar tarayya ta gayyaci Ministan Niger Delta kan badakalar NDDC

Kwamitin da majalisar tarayya ta kafa don bincike kan badakalar da aka tafka a hukumar NDDC ya bukaci Ministan harkokin Nigeri Delta, Godswill Akpabio da ya bayyana gabansa kafin karfe 11 na safiyar ranar Litinin.

A wani labarin makamancin wannan kuwa, Tsohuwar MD ta hukumar Niger Delta, Joy Nunieh, ta fayyace gaskiya gaban majalisar tarayyar kan binciken badakalar da aka tafka a hukumar NDDC.

Daga ranar Alhamis ne binciken da akeyi na badakalar hukumar NDDC ya kara daukar zafi inda jami'an rundunar 'yan sanda suka mamaye gidan Nunieh da ke Fatakwal.

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda ya hana jami'an 'yan sandan awon gaba da Nunieh, ya bukaci Sifeta Janar na rundunar, Mohammed Adamu, da ya binciki lamarin.

Akwai zargin da akeyi na cewar 'yan sandan sun mamaye gidan Nunieh ne domin hanata barin Fatakwal zuwa Abuja inda zata fayyace gaskiya gaban kwamitin binciken.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Joy Nunieh ta fayyacewa majalisar tarayya gaskiya kan badakalar NDDC

Yanzu: Majalisar tarayya ta gayyaci Ministan Niger Delta kan badakalar NDDC
Yanzu: Majalisar tarayya ta gayyaci Ministan Niger Delta kan badakalar NDDC Source: Twitter
Asali: UGC

A Abuja, manyan jami'an hukumar NDDC, da suka bayyana gaban kwamitin bincikensa sun fice daga zauren inda suka bukaci shugaban kwamitin, Mr Olubunmi Tunji-Ojo ya yi murabus

A baya bayan nan, Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktar hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta (NDDC), ta zargi Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta da damfara.

Nunieh ta zanta da manema labarai bayan bayyana da tayi a gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar dattawa a kan bincikar NDDC.

Akpabio da Nunieh sun bayyana a gaban majalisar ne yayin da ake zargin watanda da N40 biliyan da kwamitin rikon kwarya na NDDC yayi.

A yayin sauraronsu, Akpabio ya ce bai san tsarin ayyukan NDDC ba a zamanin Nunieh saboda ta ki yi mishi bayanin komai.

Amma Nunieh wacce ta jero wasu zarge-zarge a kan Akpabio, ta ce ministan ya tsigeta ne saboda ta ki bashi hadin kai.

Ta zargi cewa, Akpabio ya bukaceta da ta canja dalolin da ke asusun bankin NDDC zuwa naira, ta kori shugaban tawagar lauyoyin hukumar wanda dan arewa ne.

Sannan cewa ta cire dukkan daraktocin da suka ki bin umarninsa tare da yi wa Peter Nwaoboshi sharri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel