Ba zan lamunci cin zarafin 'yan majalisar tarayyata ba - Buhari

Ba zan lamunci cin zarafin 'yan majalisar tarayyata ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, ya ja kunnen dukkan wadanda ya nada a kan cewa ba zai lamunci rashin da'a ga majalisar tarayyar sa ba.

Kamar yadda takardar ta fito daga hannun mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa a kan yada labarai, Garba Shehu, shugaban kasar ya bada wannan jan kunnen bayan karbar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Idan za mu tuna, majalisar dattawa da karamin ministan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo, sun yi kaca-kaca a kan bayanin ayyuka 774,000.

Keyamo da 'yan majalisar sun yi kaca-kaca a yayin bayani game da kasafin aikin.

Amma kamar yadda takardar tace, Buhari ya bukaci ministoci, shugabannin sashe da cibiyoyi da su kama kansu don ba zai amince ana cin zarafin 'yan majalisar tarayyarsa ba.

Takardar ta ce, "A yayin tattaunawarsu, an bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin abubuwan da ke faruwa kuma shugaban kasar ya jaddada mutuncin majalisar tarayyarsa. Ya ce duk wani cin zarafinsu da za a yi, ba zai lamunta ba.

KU KARANTA: Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa

"Ana shawartar dukkan ministoci da shugabannin sassa da cibiyoyi a kowanne lokaci da su dinga kama kansu ta yadda ba za su dinga cin fuskar kowa ba."

Tun farko, Lawan da Gbajabiamila a wata tattaunawa da manema labaran gidan gwamnati, sun ce majalisar tarayya ba za ta amince da wani rashin da'a daga jami'an gwamnati ba.

Lawan, wanda ya yi magana a gaban Gbajabiamila, ya ce majalisar tarayya a halin yanzu na da dangantaka mai karfi da sauran jami'an gwamnati.

Ya ce, "Idan an nada ka wani mukami, kamata yayi ka yi koyi da halin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yadda yake alaka da majalisar dattawan."

A wani labari na daban, alakar da ke tsakanin ma'aikatar kwadago da majalisar dattawan kasar nan ta sake tabarbarewa a ranar Laraba a yayin da wasu wakilan majalisar da ministan kwadago, Chris Ngige suka samu rashin jituwa.

Rikicin ya fara ne bayan babban darakta a ma'aikatar kwadagon, Eyewumi Neburagho, wanda ya wakilci ministan aka gayyacesa don yin tsokaci a kan wata doka.

Kalamansa sun tada kura bayan da ya bukaci a dakatar da jin ta bakin jama'a tare da dokar har zuwa lokacin da kwamitin majalisar za su gayyaci ma'aikatar tare da tura mata dokar a rubuce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel