Kungiyar Musulmi za ta buɗe sabuwar Jami'a a Abuja

Kungiyar Musulmi za ta buɗe sabuwar Jami'a a Abuja

Wata Cibiyar addinin Musulunci MCC (Muslim Community Center), ta ba da shawarar kafa Jami'ar Tarihi a garin Bwari na birnin Abuja.

A cikin wata sanarwa, mamba a kwamitin tsare-tsare na Jami'ar ta MCC, Farfesa Isma'il Junaidu, ya ce an gabatar da takardu na kafuwar Jami'ar mai zaman kanta ga mahukuntan da suka dace.

Farfesa Junaidu ya ce sabuwar jami'ar ta gabatar da duk wasu takardu na assasa ta ga Sakataren Hukumar da ke sa ido kan Jami'o'in Kasar (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed.

Ya ce hakan ya tabbata ne ta hannun shugaban kwamitin tsare-tsaren kafa sabuwar Jami'ar, Farfesa Isma'ila A. Tsiga a ranar 8 ga Yuli a Abuja.

Farfesa Junaidu ya ce cibiyar yayin gabatar da tsarin kafa sabuwar Jami'ar, ta yi la’akari da kwarewarta wajen samar da ci gaban ilimi, musamman a Abuja.

Yayin gabatar da daftarin neman izinin kafa Jami'ar
Hoto daga Daily Trust
Yayin gabatar da daftarin neman izinin kafa Jami'ar Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Haka kuma ya ce MCC ta yi la'akari da yadda bukatar samar da ilimi a mataki na gaba da makarantun sakandire ya tsananta tare da hangen nesa wajen tabbatar da kyawawan tsare-tsare.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an dauki shawarar kafa jami'ar ne tun a shekarar 2012, tare da bibiyar duk wasu tsare-tsare da suka dace gami da yadda za a cika sharudan Hukumar NUC.

Ya ce ya zuwa yanzu, MCC ta sayi fili mai girman hekta 100 a garin Bwari tare da samun takardun shaidar mallakar filin, yayin da kuma ta ke ci gaba da bijiro da kundin tsari na dokokin Jami'ar.

A cewarsa, an kafa Cibiyar MCC ne tun a watan Nuwamban shekarar 1991, kuma an yi mata rajista a matasayin kungiyar damuwa da al'amuran Musulmi.

KARANTA KUMA: Bayar da belin wanda ake zargi da sanya wa Zainab Aliyu ƙwaya a jaka bai yiwa Hukumar NDLEA dadi ba

Ya ci gaba da cewa, daga cikin manyan akidun Cibiyar shi ne samar da wata babbar Cibiyar Ilimi da Zamantakewa domin dukkanin Musulmi.

Cibiyar mai tushe ta kunshi kwamitin amintattu da kuma majalisar zartarwa da za su rika fidda manufofi da tsare-tsare da kuma lura da duk wata gudanarwarta.

An tsinto mambobin kwamitin da kuma na majalisar daga ƙwararru a fannin Ilimi, tattalin arziki, gine-gine, injiniyanci da sauransu, waɗanda dukkansu masu aikin sa kai ne ba tare da an biya su ba.

Cibiyar MCC tana da wata makarantar sakandire ta Musulmi mai suna Fou’ad Lababidi Islamic Academy, wadda aka kafa ta a shekarar 1995 a birnin Abuja. Ta na da fiye da dalibai 1,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel