Bayar da belin wanda ake zargi da sanya wa Zainab Aliyu ƙwaya a jaka bai yiwa Hukumar NDLEA dadi ba

Bayar da belin wanda ake zargi da sanya wa Zainab Aliyu ƙwaya a jaka bai yiwa Hukumar NDLEA dadi ba

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta fusata kan hukuncin da kotu ta zartar na bayar da belin wanda ake zargi da sanya wa Zainab Aliyu ƙwaya a jaka.

NDLEA ta ce ko kadan wannan lamari bai yi mata da dadi ba a yayin da ta ke ci gaba da sa ƙafar wando daya dak duk wadanda suka ta'allaka da sha ko safarar miyagun ƙwayoyi.

Shugaban hukumar reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul, shi ne ya zayyana haka a yayin halartar wani shiri na Gidan Rediyon Freedom mai taken Barka da Hantsi.

A yayin bayyana ire-iren kalubalen da suke fuskanta, babban jami'in na hukumar NDLEA ya ce wasu alkalai na bayar da gudunmuwar da ke ta'azzara yawaitar sha da fataucin muggan ƙwayoyi a jihar.

Zainab Aliyu
Hoto daga jaridar The Punch
Zainab Aliyu Hoto daga jaridar The Punch
Asali: Facebook

Idan ba a manta ba, Hukomomin Saudiyya sun kama Zainab, dalibar jami'ar Maitama Sule dake Kano, a ranar 26 ga watan Disamban 2018 bisa zarginta da shiga da jaka dauke da ƙwayar 'tramol'.

Matashiyar ta tashi zuwa kasar Sauddiya daga filin jirgin sama na Mallam Aminu domin gudanar da aikin 'umra' tare da mahaifiyarta, Maryam, da 'yar uwarta, Hajara.

A watan Afrilun 2019 ne hukumomin Saudiyya suka saki Zainab bayan ta shafe kusan watanni 6 a gidan yarin kasar.

Haka ya biyo bayan fadi-tashin da gwamnatin Najeriya da kuma kungiyoyi masu kare hakkin bil Adama suka yi, inda aka gano cewa Zainab ba ta laifi.

Kiris ya rage gwamnatin Saudiya ta aikata lahira ta hanyar rataya kamar yadda dokar kasar ta yi tanadi ga duk mahalukin da aka kama da irin wannan laifi.

KARANTA KUMA: Kotun ECOWAS ta ci tarar Gwamnatin Tarayya N50 kan danne hakkin Alkalin Abuja

Bayan an kai ruwa rana wajen gano cewa cushen ƙwayar aka yi mata a cikin jakarta ba tare da saninta ba, Zainab ta shaki iskar 'yanci, lamarin da ya farantawa daukacin al'umma a kasar nan.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a shekarar da ta gabata ne Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Zainab kyautar Naira miliyan 3 bayan an dawo da ita Najeriya.

Ganduje ya ba ta kyautar wannan kudi domin rangwanta mata radadi na halin kunci da ta fuskanta yayin kasancewar ta a gidan cin sarka.

Ganduje ya yi godiyar ta musamman ga dukkanin wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin Zainab ta shaki iskar 'yanci musamman mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin 'yan Najeriya mazauna ketare, Abike Dabiri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng