Majalisar Dattawa ta amince da kudirin buɗe sabbin jami'o'i a Najeriya

Majalisar Dattawa ta amince da kudirin buɗe sabbin jami'o'i a Najeriya

Mun samu rahoton cewa za a buɗe sabbin jami'o'in Tarayya biyu da kuma Kwalejin Ilimi ta Tarayya domin bunkasa ilimi da zai tabbatar da ci gaba a kasar Najeriya.

Majalisar Dattawa ta amince da kudirin kafa Jami'ar Fasaha ta Tarayya a Auchi, Jihar Edo da kuma wasu Jami'o'i biyu a fadin kasar.

Ta biyu da Majalisar ta amince da kudirin buɗe su sun hadar da Jami'ar Harkokin Jiragen Ruwa ta Najeriya a Okerenkoko a Jihar Delta.

Za kuma a kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Karamar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna.

Majalisar ta amince da wannan kudiri yayin zaman da ta gudanar a ranar Laraba, bayan kammala karatu a kan kudirin kafa manyan makarantun na gaba da sakandire.

Zauren Majalisar Dattawa
Hoto daga NigerianSenate
Zauren Majalisar Dattawa Hoto daga NigerianSenate
Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin majalisar mai kula da Makarantun Gaba da Sakandire da Asusun Tallafa wa Jami'o'i (TETFUND) wanda Sanata Babba Kaita ya gabatar.

Sanata James Manager na jam'iyyar PDP mai wakiltar shiyyar Delta ta Kudu a majalisar, shi ne ya gabatar da kudurin kafa Jamiar Harkokin Jiragen Ruwa ta Najeriya

Sai kuma Sanata Uba Sani daga jihar Kaduna ya gabatar da kudurin kafa Kwalejin Ilimi a Giwa yayin da Sanata Francis Alimikhena daga jihar Edo ya gabatar da kudurin kafa Jami'ar Fasaha ta Auchi.

KARANTA KUMA: Fulanin Daddo Pulaku sun bukaci kashi 4% na filaye a Bauchi domin dakile rikicin makiyaya da manoma

A yayin gabatar da rahoton, Sanata Kaita ya ce akwai bukatar a daga likafar Kwalejin Tarayya ta Auchi domin da zama Jami'a mai cin gashin kanta.

Ya ce Kwalejin (Federal Polytechnic Auchi) ta na gudanar da kwasa-kwasai daban-daban na digiri a yayin da take da alaƙa da Jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke birnin Awka a jihar Anambra.

Haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin jihar Gombe ta shirya fara bada shaidar karamci daga hukumar kula da harkokin karatun Arabi da addinin Musulunci ta kasa (NBAIS) ga mahaddata Al-Qur'ani..

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Dr. Abdullahi Bappah Ahmad Garkuwa, jami'in gudanar da shirin samar da nagartaccen ilimi ga kowa na jihar Gombe (BESDA).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng