Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun zagaye gidan tsohuwar MD ta NDDC

Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun zagaye gidan tsohuwar MD ta NDDC

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun tsinkayi gidan Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar habaka yankin Neja Delta (NDDC), inda suka yi masa zobe.

Jami'an tsaron sun isa gidan ne da ke lamba 3, titin Owuru Creek, kusa da titin Herbert Macauley da ke tsohuwar GRA a Fatakwal, jihar Ribas a sa'o;in farko na ranar Alhamis.

Wannan ci gaba ya faru ne kafin isar Nunieh gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa da ke Abuja inda za ta amsa tambayoyi a kan ayyukan NDDC.

A yayin da jaridar The Cable ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Omoni Nnamdi don tsokaci, ya bukaci a kira sa nan da mintuna 30.

Akpabio da Nunieh sun bayyana a gaban kwamitin rikon kwarya na majalisar dattawa, inda ake bincikarsa a kan badakalar wasu kudade har N40 biliyan wanda kwamitin rikon kwarya na hukumar suka lamushe.

A yayin sauraronsu, Akpabio ya ce bai san tsarin kudin kashewa na NDDC ba karkashin Nunieh saboda bata bashi bayanin da ya kamata.

Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun zagaye gidan tsohuwar MD ta NDDC
Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun zagaye gidan tsohuwar MD ta NDDC. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar dattawa ya yi watsi da sallamarsa da aka yi

Amma kuma Nunieh ta ce ministan ya tabbatar da tsigeta ne saboda ta ki yin abinda yake so.

Tsohuwar manajan daraktar NDDC ta bayyana zargi kala-kala game da ministan. Ta zargesa da yunkurin lalata da ita.

Nunieh ta zargi ministan da umartar ta da ta canza kudin asusun NDDC daga dala zuwa Naira. Ya bata umarnin sallamar shugaban lauyoyin hukumar saboda dan arewa ne.

Ta zargesa da bata umarnin cire dukkan daraktocin da suka ki bin umarninsa tare da lakabawa Peter Nwaoboshi, shugaban kwamitin NDDC na majalisar dattawa sharri.

Ta kara da cewa Akpabio ya bada kwangila 30 kafin ta zama mukaddashin shugaban hukumar.

Gwamnatin jihar Ribas ta yi kira ga Akpabio, inda ta ja kunne cewa kada wani abu mai muni ya fada wa Nunieh, wacce gwamnatin ta kwatanta da diyarta.

A yau ne Joy Nunieh da Godswill Akpabio za su bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa don amsa tambayoyi a kan N40 biliyan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel