Muƙamai da albashin ma'aikatan 'yan sanda a Najeriya
A ranar Asabar ne rundunar 'yan sandan Nigeria ta sanar da shirinta na neman daukar ma'aikata a rukunin shekarar 2020.
Kakakin rundunar Frank Mba ya sanar da hakan yana mai cewa rundunar zata dauki mutanen da suka cancanta a mukamin kwanstabul, daga watan Yuli zuwa watan Agusta.
Frank Mba ya ce za a gudanar da matakan daukar aikin ne ta hanyar shigar da bayanai a shafin hukumar na yanar gizo.
Ya bukaci masu sha'awar neman aikin da su ziyarci adireshin hukumar www.policerecruitment.gov.ng domin cike dukkanin bayanan da ake bukata.
Mba ya yi nuni da cewa dole ne masu son neman aikin su cika duk wasu ka'idoji da aka zayyana a shafin hukumar na yanar gizo.
Ya ce za a gayyaci wadanda suka yi nasara zuwa tantancewa ta zahiri a manyan ofisoshin hukumar dake fadin jihohin kasar da suka hada babban ofishin hukumar na Abuja, daga ranar 24 ga watan zuwa 30 ga watan Agusta 2020.
Mai magana da yawun rundunar ya ce za a manna sunayen wadanda suka samu nasarar tantancewar a manyan jaridu na kasa a ranar 14 ga watan Satumba 2020 da kuma shafin hukumar na yanar gizo.

Asali: Twitter
A wani rahoto da sashen Hausa na BBC ya ruwaito dangane da ababen da ya kamata a sani game da aikin ɗan sanda. Daga cikin abubuwar da jaridar ta fito da su fili sun haɗar da albashi da kuma makaman jami'an hukumar.
Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi, hukumar 'yan sanda ita ce babbar hukumar da ke tabbatar da tsaro da kiyaye doka a kasar.
KARANTA KUMA: Kudin horar da Jami'ai: An titsiye Magu kan N700m da ta ɓata a hukumar EFCC
Jagoran hukumar shi ne Babban Sufeton 'Yan Sanda na Najeriya. Su na da kwamishinoni a jihohi 36 da ke fadin kasar da kuma babban birnin tarayya.
Kamar yadda mai magana da yawun hukumar a reshenta na jihar Ogun, Abimboa Opeyemi ya zayyana, ana shiga aikin dan sanda domin kishin kasa ba don neman kudi ba.
Ga albashin 'yan sandan Najeriya:
Kurtu: N46,000 zuwa N47,000
Kofur: N52,000-zuwa N53,000
Sajan: N62,000 zuwa N63,000
Mai anini 1: N78,000
Sufeto Anini 2: N123,000
ASP Mai Tauraro 1: N132,000 zuwa N134,000
ASP: N139,000
DSP: N142,000 zuwa N143,000
SP: N161,000 zuwa N187,000
CSP: N172,000 zuwa N199,000
ACP: N183,000 zuwa N212,000
DCP: 242,000 zuwa 278,000
CP: N266,000 zuwa 302,000
AIG: N499,000
DIG: N546,000
IGP: N711,000
Ga kuma jerin duk muƙaman 'yan sandan Najeriya
Babban Sufeto Janar - Inspector General of Police (IGP)
Mataimakin Sufeto Janar na 'yan Sanda (DIG)
Mataimakin Sufeto Janar na 'yan Sanda (AIG)
Kwamishinan 'Yan sanda (CP)
Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (DCP)
Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (ACP)
Babban Sufiritandan 'Yan Sanda (CSP)
Sufritandan 'Yan Sanda (SP)
Mataimakin Sufiritandan 'Yan Sanda (DSP)
Mataimakin Sufiritandan 'Yan Sanda (ASP)
Sufetan 'Yan Sanda (Inspector of Police)
Samanja
Saje
Kofur
Las Kofur
Kurtu
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng