Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida

Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida

- Jami'an tsaro sun samu gawar matashin dan kasuwa, Fahim Saleh a gidansa da ke birnin New York

- Kamar yadda New York Daily Times ta wallafa, matashin ne mamallakin kamfanin babura na GoKada

- An samu gawar shi ne bayan an yi gunduwa-gunduwa da ita, lamarin da ke nuna cewa kashe shi aka yi har lahira

An samu gawar mamallakin babban kamfanin babura na 'GoKada', Fahim Saleh a gidan sa da ke birnin New York.

Kamar yadda jaridar New York Daily Times ta wallafa, an samu gawar dan kasuwar wacce aka yin gunduwa-gunduwa da ita da ranar Talata.

Wani jami'in NYPD ya ce masu bincike sun tabbatar da cewa wannan gawar ta Fahim Saleh ce mai shekaru 33 wanda ya siya condo a dala 2.25 miliyan a shekarar da ta gabata.

Kakakin NYPD, Sajan Carlos Nieves ya ce an samu dukkan sassan jikinsa a wurin da abun ya faru amma sun ki bada tabbaci a kan wurin.

Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida
Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida. Hoto daga The Cable
Asali: Instagram

KU KARANTA: Matar aure ta kashe aurenta bayan cewa da tayi za ta iya cin amanar mijinta a kan N200,000

Kamfaninsa ya fuskanci ci baya a yayin da jihar Legas ta haramta ayyukan babura a wasu sassanta a watan janairun 2020.

NYPD ta ce ta samu wani sako kusa da gawar hamshakin mai kudin, jaridar Daily Mail UK ta wallafa.

'Yan sandan sun ce sun yi wannan gamon da gawarsa ne a hawa na bakwai na wani gini da ke E' Houston wurin karfe 3:30 na ranar Talata bayan daya daga cikin 'yan uwansa ya kira 911 saboda bai gan shi ba dukkan yinin.

An ga Saleh a ranar Litinin da ta gabata wurin karfe 1:40 na rasa, kamara yadda CCTV ta nada. An gano cewa ya shiga na'urar rage nisan hanya da wanda ake zargin ya kashesa.

Bidiyon ya nuna yadda wanda ake tsammanin ya kashesa yana biye da shi da jaka har zuwa cikin na'urar kuma ya fara aiwatar da mugun aikinsa a lokacin da suka kai hawa na bakwai.

An samu jakar a kusa da gangar jikinsa da aka yi gunduwa-gunduwa da ita amma 'yan sanda basu bude jakar da gaggawa ba.

An cire hannayensa tare da kafafunsa kuma an saka sauran sassan jikinsa a wata jaka ta roba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel